✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Samar da tsaro: Zamfarawa 3,850 sun fara samun horo

An fara horas da rukunin farko na mutum 7,500 da za su yi aikin samar da tsaro a Zamfara

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Zamfara ta tura mutum 3,850 da za a horas kan samar da tsaro a cikin al’ummomin jihar.

Jami’an tson da za su yi aiki tare da ’yan sanda sun tafi makarantun horas da kuratan ’yan sanda da ke Kaduna da Sakkwato domin samun horo na tsawon wata biyu kafin su fara aiki a al’ummominsu a watan Disamba.

“Jihar Zamfara ce a fadin Najeriya ta fara daukar wannan gagarumin mataki.

“Samar da jami’an tsaron zai taimaka gaya wajen kawo tsaro a kasa, domini idan Jihar Zamfara ta samu tsaro to Arewacin Najeriya da ma kasar sun samu”, a cewar Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Zamfara, Usman Nagogo Gabanin tafiyar jami’an zuwa cibiyoyin horaswan.

Kamishinan ya ce matasan su ne rukunin farko na mutum 7,500 da Gwamna Muhammad Matawalle ya samu sahalewar Shugaban ’Yan Sandan Najeriya, Mohammed Adamu a dauka domin samar da tsaro a al’ummomi wadanda Gwamnanin Zamfara za ta rika biyan su albashi.

“Kwamitocin amintattun mutanen a kananan hukumomi ne suka zabo tare da tantace jami’an na musamman.

“Za su rika sanya kaki daban da na ’yan sandan wanda ’yan sanda ne za su san bambancin, sannan za su rika aiki ne tare da mu a wuraren da muke aiki”, inji shi.

Ya ce hikimar sanya su samar da tsaron shi ne sun fahimci yanayin al’ummominsu da suka taso a ciki kuma za su fi saurin gano take-taken bata-gari da kuma magance su da sauri.

Sai dai ya ce rundunar ba za ta lamunci karbar rashawa ko cin dunduniyarta ba, kuma duk wanda aka kama zai dandana kudarsa.