✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sojoji sun kashe mayakan Boko Haram da dama a Borno

Dakarun rundunar sojojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole sun tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda tare da kashe wasu da dama

Dakarun rundunar sojojin Najeriya ta Operation Lafiya Dole sun tarwatsa maboyar ‘yan ta’adda tare da kashe wasu da dama daga cikinsu a garunruwan Ngwuri Gana da Jumacheri a jihar Borno.

Garin dai na Ngwuri Gana na kan hanyar Gulumba Gana-Kumshe yayin da shi kuma Jumacheri ke kusa da garin Damasak na arewacin jihar Borno.

Rahotanni sun nuna cewa an yi amfani da jiragen yakin Rundunar sojin Saman Najeriya da wani jirgin mai saukar ungulu a yankunan wajen kai harin tare da tarwatsa maboyar ‘yan ta’addan sannan aka kashe gwammai daga cikinsu.

Jami’in sashen dake samar da bayanai kan ayyukan rundunar, Manjo Janar John Enenche shine ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya rabawa ‘yan jarida ranar Lahadi.

Enenche ya ce, “Mun sami wannan gagarumar nasarar ce sakamakon wasu jerin hare-hare da dakarunmu suka kai ranar 21 da 22 ga watan Oktoban 2020 bayan samun wasu bayanan sirri da suka nuna cewa ‘yan ta’adda da dama sun yi sansani a wuraren a kokarin da suke yi na kaiwa rundunoninmu dake da makwabtaka da su hari.”

A ‘yan kwanakin nan dai sojojin sun tarwatsa kusan akalla maboyar ‘yan ta’addan guda 10 a sassa da daman a kusa da yankin Tafkin Chadi.