Search
Subscribe
Sojoji sun kwato mutumm 17 a hannun ‘yan bindiga

Sojoji sun kwato mutumm 17 a hannun ‘yan bindiga

Mutum 17 sun kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane bayan wani samame da sojoji suka kai a Jihar Zamfara.

Mutanen da aka kubutar daga hannun masu garkuwan ‘yan asalin jihar Sokoto, kuma an hannanta su ga gwamnatin jiharsu.

Da yake karbar su, Gwamna Aminu Tambuwal ya yi farin cikin kasancewarsu cikin koshin lafiya tare da godiya ga Gwamnatin Zamfara a kan kokarin.

Tambuwal ya kuma jaddada kiransa ga jama’ar jihar Sokoto da su ba wa jami’an tsaro hadin kai wurin yakar ‘yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

A cewarsa, gwamnatinsa a shirye ta ke da ta tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a jihar.

Kwamishina samar da ayyuka da tsaron jihar Sokoto, Garba Moyi, ya ce 16 daga cikin wadanda aka kubutar sun fito ne daga Karamar Hukumar Tureta, mutum daya kuma daga Rabbah.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin