✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Soyayyar badala: Shawarar da uwa ta ba diyarta

Tare da sallama, da fatan na same ku lafiya, bayan hutun wata daya cur da na yi. A sha ruwa a koma aiki, inji Hausawa,…

Tare da sallama, da fatan na same ku lafiya, bayan hutun wata daya cur da na yi. A sha ruwa a koma aiki, inji Hausawa, don haka mun dawo wannan fage don ci gaba da fantamawa cikin lambun soyayya. A wannan makon wani labari ne mai kidimarwa kuma mai dauke da muhimmin darasi ya shiga komata. Ina kishingide, sai kawai na ci karo da wannan labari, wanda Malam Nasir G. Ahmad Kano 08098559946 ya rubuta. Ni kuwa FDk (Filfilon Dausayin kauna) na ce ba zan kyale shi haka nan ba, sai masoya sun ji shi. Ga labarin: