✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rashin lantarki da tsadar fetur ke kassara masana’antu

A yanzu saboda ƙarin kuɗin da muka yi cinikin ruwa ya yi baya sosai. Mutane sun rage sayen fiya-wata.

Masu kanana da matsakaitan masana’antu da harkokin kasuwanci suna ci gaba da kokawa kan munin karancin wutan lantarki da ake ciki wanda ya fara tun dawowa hutun karshen shekara.

Masu sana’antun roba da na ruwan leda da ajiyar kifi da wanda na kan gaba wajen fuskantar matsalar, haka ma teloli da masu injunan niƙa da surfe.

Idan ba a manta ba, bayan janye tallafin man fetur, farashinsa ya tashi sama, inda ya shafi harkokin yau da kullum.

Kuma masu kananan sana’o’i da kasuwanci da dama sun dogara ne da ko dai wutar lantarki, ko kuma janareta domin gudanar da harkokinsu.

Matsalar wutar lantarki ba sabuwar aba ba ce a Nijeriya, hakan ya dade yana ci wa masu kananan sana’o’i tuwo a kwarya, sai dai yadda lamarin ya tabarbare a daidai lokacin da man fetur ya cilla sama hakan na kassara masu kananan masana’antu da sana’o’i.

A baya wasu masu sana’ar sun fi samun kwanciyar hankali aikin da janareta, wanda yanzu zai yi wahalar gaske saboda tsadar fetur din.

Wani mai harkar sarrafa roba a Unguwar Kaduna Road da ke garin Suleja a Jihar Neja, Malam Abubakar Baba Abdullahi ya ce a yanzu ba sa samun wutar lantarkin da ta wuce awa 4 daga cikin awa 24, sabanin shekarun baya lokacin da suke samun ta awa 18.

Ya ce hakan ya sa aikinsu ya ja baya kuma a dalilin haka suka rage ma’aikatan da suke karkashinsu.

Ya ce a baya a masana’antar roba daya ana samun ma’aikata kamar 60 da suka shafi masu tantance nau’o’in roba da masu nika ta, sai mata masu wankewa suna wanke nikakkiyar robar kafin wasu su narka ta.

Ya ce hakan na faruwa ne a lokacin da aka kara kudin wutar lantarki da tsadar kayan sauke ta kamar falwaya da waya da mitar wutar.

Malam Abubakar Baba Abdullahi ya bukaci gwamnati ta sake waiwayar kamfanonin da ta yi gwanjonsu na tashoshin wutar lantarki da rarraba ta, wadanda ya ce sun gaza “Kusan kamfanonin tatsar kudi kawai suke yi daga jama’a ba tare da inganta wutar lantarkin daga matakin da suka same ta ba.

“Yawanci wayoyin da ake amfani da su wajen kai wutar lantakin sun gaza wasu sun lalace ba sa iya daukar nauyin wutar lantarkin da ake turawa ta kansu.

“Dole ne gwamnati ta binciki lamarin idan ba za su iya ba, a soke cinikin,” in ji mai kamafanin sarrafa robar.

Shi ma a zantawa da Aminiya, wani mai masana’antar ruwan roba da ke garin Dutsen Alhaji a yankin Birnin Tarayya, Abuja, Malam Dauda Umar ya ce yawanci wutar lantarkin na zuwa masu ne da tsakar dare a yanzu inda ake daukewa bayan awa biyu sannan a sake dawo da ita kafin wayewan gari, sai kuma wani lokaci da tsakar rana.

Ya ce adadin wutar lantarkin da ake bayarwa a yankinsu ba ta wuce ta awa shida zuwa bakwai daga cikin awa 24.

Ya ce lamarin ya kara muni ne a mako biyu zuwa yanzu sabanin watannin baya lokacin da ake samun wutar na kimanin awa 20 daga cikin awa 24.

Ya ce wasu daga cikinsu da suke amfani da janaretoci masu amfani da man fetur ko gas na kashe mafi yawan abin da ya kamata ya kasance ribarsu wajen sayen mai.

“A yanzu litar gas ta kai Naira 1,600, ka ga jarkar mai mai lita 20 na kai Naira dubu 32 ke nan, kuma idan ka fara aiki da shi ba lallai ba ne ya kai ka awa 32, ka gaya mini yadda za ka samu riba a kai,” in ji shi.

Malam Dauda Umar ya ce akwai yankunan garin da matsalarsu ta dara haka muni inda ya yi misali da wata unguwa da ta fuskanci matsalar lalacewar taransfoma sama da wata hudu.

Dama su ne suka sayi na’urar a baya kuma bayan lalacewarta kamfanin ya kasa gyara musu na’urar haka ake zaune a yankin babu wuta a tsawon wannan lokaci.

Akwai yiwuwar karin kudin dinki dalilin matsalar — Ibrahim Tela

Wani mai sana’ar dinki a garin Kubwa da ke Birnin Tarayya Abuja Malam Ibrahim Muhammad ya ce akwai yiwuwar karin kuɗin dinki a kakar aikinsu na watan azumin bana a dalilin matasalar wutar lantarkin kawai.

Ya ce hakan na faruwa ne a lokacin da kudin kayan aiki ya ninka sama da biyu.

Ya ce kayan aiki da suke saya Naira 500 a yanzu wani ya kai Naira 1,500.

Ya ce hakan ya sa kudin da yake rage masu bayan sayayyar kayan aiki a yanzu na karewa ne a wajen sayan mai.

“To zai yi wuya mu tsira da wani abu a haka, ka ga ke nan dole mu yi karin kudi, musamman kan matsalar karancin wuta ba ya ga ta tsadar rayuwa,” in ji Malam Ibrahim.

Duk da cewa wannan matsala ce da ta shafi kowa, sai dai za a iya cewa kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i a Jihar Kano sun fi kowa karbar gashi saboda lamarin ya shafi harkokinsu.

A bayan nan kuma sakamakon tashin farashin kayayyaki a kasar nan ita kanta wutar lantarki wacce ba samuwa take yi a koyaushe ba, an samu kari a kudinta.

Farashinta ya yi tashin gwaron zabo idan aka dauki masu amfani da mita wacce ake sa kati za a tarar kudin kowane yunit ya karu.

Za a iya cewa a yanzu rashin wutar da tsadarta na janyo wa kananan ’yan kasuwa da masu sana’o’i durkushewa saboda da dama daga cikinsu sun rufe wuraren harkokin nasu, saboda maimakon su kirga riba sai faɗuwa suke kirgawa.

Malam Nasiru Umar wani mai sana’ar dinki a Kano ya ce kasancewar a yanzu ba a samun wutar lantarki a kasa ya sa sana’arsa ba ta tafiya yadda ta kamata.

“A yanzu ba mu samun wutar lantarki a unguwarmu, hakan ya janyo ba na iya dinki mai yawa kamar yadda na saba. Kin san keken da muke amfani da shi na lantarki ne.

“Idan za ka dinka riga uku a rana ta hanyar yin amfani da keken da ba na lantarki ba, to, za ka iya dinka riga bakwai zuwa goma da keke mai amfani da lantarki.

“Yanzu kuma ga tsadar man fetur wanda idan mutum ya ce da shi zai yi amfani, to fa ba zai gane komai a harkar ba.

“Saboda mutane ba za su iya biyan kudin da za a nemi su biya ba idan an yi musu dinki da man fetur,” in ji shi.

A cewar telan ba ya da zabi a yanzu illa ya koma amfani da keken da ba ya amfani da lantarki wanda kuma ba ya da sauri wajen aiki.

Ya ce “Kin ga hakan gurguncewar sana’ata ce domin ba zan iya dinka dukkan kayan da aka kawo min kafin Sallah ba.”

Alhaji Bashir Haruna ya bayyana cewa a halin yanzu suna fuskantar koma baya a sana’arsa ta kayan sanyi sakamakon tsadar wutar lantarki.

“A yanzu sakamakon halin da aka shiga na karin kudin wutar lantarki ba mu yin ciniki kamar yadda muka saba a baya.

“Na farko ga shi an samu karin farashin kayayyakin da ake amfani da su wajen yin fiyawata musamman leda.

“Baya ga rashin wutar lantarki da muke fama da shi, sai ga shi kuna an samu karin kudin wutar lantarkin kanta.

“A duk lokacin da ba wutar lantarki mukan yi amfani da man dizal wanda kowa ya san tsadarsa a yanzu.

“Hakan ya janyo muka yi ƙarin kuɗin ruwa daga Naira 100 zuwa Naira 170 a kan kowacce leda,” in ji shi.

Ya ce ƙarin kuɗin da suka yi ya janyo cinikin ya yi kasa. “A yanzu fa saboda ƙarin kuɗin da muka yi cinikin ruwa ya yi baya sosai. Mutane sun rage sayen ruwan ‘fiya-wata,” in ji shi.