✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

’Yan bindiga sun kashe limani da mutum 9 a Katsina

’Yan bindigar sun kashe mutun goma ciki har da wani limamin da nai'ibinsa a Faskari, Jihar Katsina

’Yan bindiga sun kashe mutum 10 a hare-haren da suka kai a wasu kauya na Karamar Hukumar Faskari, Jihar Katsina.

Maharan sun kashe mutun takwas a kauyen Shau ciki har da limamin kauyen da na’ibinsa a ranar Lahadi.

Shaidu sun ce maharan sun shiga garin ne a kan babura suna harbe-harbe, suka jikkata mutane suka kona gidaje tare da sace shanu.

Mazaunan sun ce bayan nan ne ’yan bindigar suka far wa kauyen Ruwangodiya suka kashe mutum biyu tare da jikkata wasu da dama.

Majiyarmu ta ce mazauna garin sun tsere ba a san inda suke ba, ciki har da mata da kananan yara.

Kakakin ’Yan Sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah ya tabbatar da aukuwar lamarin.

Ya ce tuni aka tura ’yan sanda su bi sawun maharan a dazukan da ke makwabtaka da garuruwan domin a hukunta su.

SP Gambo Isa ya ce tuni al’amura suka daidaita a kauyukan biyu bayan hari da ’yan bindiga suka kai.