✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka yi jana’izar Hakimin ’Yantumaki

An yi jana’izar Marigayi Sarkin Fulanin Dangin, Hakimin ’Yantumaki, Alhaji Atiku Maidabino. Dubban jama’a ne suka halarci jana’izar hakimin a gidanshi da ke garin na…

An yi jana’izar Marigayi Sarkin Fulanin Dangin, Hakimin ’Yantumaki, Alhaji Atiku Maidabino.

Dubban jama’a ne suka halarci jana’izar hakimin a gidanshi da ke garin na ‘Yantumaki.

Alhaji Atiku Maidabino ya rasu ne sakamakon harbi shi da wasu ‘yan bindiga suka yi mishi a gidansa da daren Lahadi.

Mai Martaba Sarkin Katsina Alhaji Abdulmumin Kabir Usman yana cikin wadanda suka halarci jana’izar tare da hakiman Masarautar ta Katsina da dama.

Sakataran Gwamnatin jihar Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa, da kwamishinan kananan hukumomi da masarautu, Alhaji Yau Umar Gwajo Gwajo ma sun halarci jana’izar.

Sauran wadanda suka kasasnce a wurin sun hada da babban sakataren ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar Katsina, Abubakar Ahmad ‘Yantumaki, tare da dan majalisar jihar mai wakiltar karamar hukumar Danmusa, Hon Aminu A Garba, da kuma da yawa daga jami’an gwamnatin jihar da sauran al’umma.