✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan Najeriya 23,000 sun yi gudun hijira zuwa Nijar —Rahoto

An kiyasta cewa kimanin ’yan Najeriya 23,000 ne suka shiga Jamhuriyar Nijar don neman mafaka sakamakon kalubalen  tsaro a wasu yankunan Arewa Maso Yamma. Kakakin…

An kiyasta cewa kimanin ’yan Najeriya 23,000 ne suka shiga Jamhuriyar Nijar don neman mafaka sakamakon kalubalen  tsaro a wasu yankunan Arewa Maso Yamma.

Kakakin Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya Babar Baloch ne ya bayyana wa manema labarai hakan a birnin Geneva, kamar yadda wata sanarwa ta nuna.

Babar ya ce wannan adadin ya sa yawan ‘yan gudun hijirar da ke tserewa daga arewcin Najeriya suna neman mafaka a Nijar ya haura 60,000 tun bayan fara kwarar su a watan Afrilun bara.

“Tun watan Afrilu 2019, jama’a da suke ta yin hijira don gujewa hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa ba kakkautawa a wasu yankunan jihohin Sakkwato da Zamfara da Katsina.

“Galibin ’yan gudun hijirar sun samu mafaka ne a Maradi”, a cewar sanarwar.

Kalubalen da Nijar ka iya fuskanta

Hukumar kula da ’yan gudun hijirar ta kuma nuna damuwa game da tabarbarewar tsaro a cikin Najeriya da kuma yiwuwar fantsamar hare-hare zuwa cikin Nijar.

Ta kara da cewa kwarar ’yan gudun hijirar ta baya-bayan nan, galibi mata da kananan yara ta biyo bayan hare-hare ne a watan Afrilu a jihohin Katsina da Sakkwato da Zamfara.

Kauyuka da yawa ne a kananan hukumomin jihohin ’yan bindiga suka kaiwa hare-hare.

Hari mafi muni da ’yan bindigar suka kai shi ne wanda ya yi sanadin salwantar rayuwkan mutum 47 a kananan hukumomin Kankara da Danmusa da Dutsin-ma duk a cikin jihar Katsina, ya kuma janyo martanin rundunar sojin saman Najeriya.

Dalilin ’yan Najeriya yin gudun hijira zuwa Nijar

“’Yan gudun hijirar sun ba da labarin munanan hare-hare a kan fararen hula da kisan gilla da sace mutane don neman kudin fansa da kona kauyuka da sace masu dukiya.

“An bai wa ’yan gudun hijirar Najeriya damar neman mafaka a Nijar duk da rufe iyakokin kasar sakamakon bullar annobar COVID-19.

“Sababbin ’yan gudun hijirar a yanzu sun fi bukatar ruwa, da abinci da kayan kayan kiwon kiwon lafiya tare da masuki da kuma tufafi.

Galibinsu sun shiga Nijar ne ba tare da wani guzuri ba”, inji sanarwar.

Hukumar ta kara da cewa wasu sun yi hijirar ne sakamakon yawan rikici tsakanin manoma da makiyaya daga bangarori daban-daban ciki har da ’yan banga.

“Kashi 95 cikin 100 na ’yan gudun hijirar sun fito ne daga jihar Sakkwato a Najeriya, yayin da sauran ’yan jihohin Kano da Zamfara da kuma Katsina ne.”