✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

’Yan sanda sun ceto yara 5 da aka yi safarar su zuwa Legas

Rundunar ta ce za ta ci gaba da bincike a kan wadda ake zargin.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, ta ceto wasu kananan yara biyar daga hannun wata kungiya da ake zargin masu safarar mutane ne da ke aiki a Jihar Kwara.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar, SP Benjamin Hundeyin, ya tabbatar wa kamfanin Dillancin Labaran Najeriya (NAN) a ranar Litinin.

Hundeyin, ya ce kananan yaran da aka ceto an mika su ga iyayensu.

NAN ta ruwaito cewa an kama wata da ake zargin ta kware wajen fataucin yara a ranar 28 ga watan Janairu, bayan da rundunar ta shafe wata uku tana nemanta ruwa a jallo.

Tun da farko Hundeyin ya shaida wa NAN cewa kungiyar ta kan yi safarar kananan yara daga Arewacin Najeriya zuwa Jihar Legas, domin yin sana’o’in hannu da sauran ayyukan da suka saba wa doka.

Ya ce a ranar 25 ga watan Janairu, wata ’yar shekara 45, mai suna Alimot Haruna da ke zaune kauyen Molete, a Ilorin, ta shiga hannun ‘yan sanda.

“An ceto yaran da ba su wuce shekara uku ba, mata biyu da namiji daya ba, sai kuma wasu masu shekara bakwai zuwa 12 – wadanda suka kasa bayyana adireshinsu.

“Lokacin da ake yi mata tambayoyi, wadda ake zargin ta amsa laifinta.

“Bincike ya nuna cewa wadda ake zargin ta yi fataucin yara 42 zuwa Legas ba bisa ka’ida.”

Hundeyin ya tabbatar da cewad rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta ceto wasu daga cikin yaran, sauran yara 11 da ake nema.

Ya ce za su ci gaba da gudanar da bincike kafin gurfanar da wadda ake zargin a gaban kotu.