✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Za a bude makarantu na musamman 5 a Kano

Kwamishinan Ilimin jihar ya ce za a rarraba makarantun ne a masarautu biyar da ke jihar

Gwamnan Jihar Kano ya amince da kirkirar sabbin makarantun sakandare na musamman Mega Unity Schools guda biyar a lokacin zamanta da ta saba gudanarwa duk Laraba.

Kwamishinan Ilimin jihar, Malam Muhammad Sanusi Sa’id Kiru, ya ce za a rarraba makarantun ne a masarautu biyar da ke jihar.

“A kokarinta na habaka bangaren ilimi ta hanyar samar da makarantu masu inganci, Gwamnatin Jihar kano ta amince da kirkirar makarantun sakandare na Mega Unity Schools (Makarantun Hadaka na Musamman) wanda za a rarraba su ga masarautun jihar biyar”, inji shi.

Kwamishinan ya kara da cewa makarantun za su fara ne da daukar dalibai 360 kowaccensu sannan za su fara da ’yan aji 1 zuwa 3 na karamar sakandare, sai kuma aji 4 na babbar sakandare, a zangon karatu na 2020/2021.

Sanusi ya ce, a yanzu makarantun hadaka na Unity School a Jihar Kano sun zama 7 ke nan idan aka hada da wadanda suke a Karaye da Kachako.

“An bude bayar da takardar neman shiga makarantun na Unity School ga jihohi 18 da suke shiyyar Yammacin kasar nan”, inji shi.

Ya ce “Jagorancin makarantun za su kasance ne karkashin ma’aikatan da suka kai matsayin Darakta da Mataimakin Darakta a matsayin Principal da mataimakinsa masu matakin albashi na 15,” a cewar Kwamishinan Ilimin.