✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zidane ya bayyana ’yan kwallon da Madrid za ta yi bankwana da su

Kocin Real Madrid da ke Sifen Zinedine Zidane ya shirya tsaf don sallamar wasu daga cikin ’yan wasan kulob din a bana. Daga cikin ’yan…

Kocin Real Madrid da ke Sifen Zinedine Zidane ya shirya tsaf don sallamar wasu daga cikin ’yan wasan kulob din a bana.

Daga cikin ’yan kwallon da kulob din zai cefanar akwai

Gareth Bale da James Rodriguez da Isco da Keylor Nabas da sauransu.

Sai dai kocin ya ce kulob din zai maye gurbin ’yan kwallon da zai sallama ne da ’yan wasa irin su Paul Pogba da Eden Hazard da Christian Eriksen da sauransu.

A bana kulob din Real Madrid bai lashe kofi ko daya ba sannan ya gama ne a matsayi na uku a gasar La-Liga ta Sifen.