✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A daukaka darajar Asibitin Kafanchan zuwa Asibitin Kwararru – Dokta Kure

Babban Daraktan Asibitin Tunawa da Patrick Ibrahim Yakowa da aka fi sani da Janaral da ke garin Kafanchan fadar Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna,…

Babban Daraktan Asibitin Tunawa da Patrick Ibrahim Yakowa da aka fi sani da Janaral da ke garin Kafanchan fadar Karamar Hukumar Jama’a a Jihar Kaduna, Dokta Samuel Maidawa Kure ya yi kira ga gwamnatin jihar ta daukaka darajar asibitin zuwa Asibitin Kwararru ko Asibitin Koyarwa ko kuma Cibiyar Lafiya ta Tarayya (FMC).

Shugaban asibitin ya yi wannan kira ne yayin tarbar ayarin Mai martaba Sarkin Jama’a Alhaji Dokta Muhammad Isa Muhammad II yayin ziyarar marasa lafiya da Sarkin ke yi lokacin Hawan Daushe, inda ya yi kira ga Sarkin ya yi amfani da matsayinsa na wanda asibitin ke zaune a masarautarsa don mika wannan bukata.

Dokta Kure ya ce yin hakan zai yi matukar amfana ba ga jama’ar masarautar ko karamar hukumar ba kawai ba har da dukkan kananan hukumomin jihar Kaduna da wasu kananan hukumomin Jihar Nasarawa da ke makwabtaka da su saboda kasancewarsa asibiti mafi girma a Kudancin Kaduna.

“Hakan zai saukaka mana tura marasa lafiya zuwa garuruwan Jos da Kaduna da Abuja wanda hakan barazana ce ga rayuwar marasa lafiyar da ke bukatar kular gaggawa ko ta musamman,” inji shi.

Shugaban asibitin ya jinjina wa Sarkin kan riko da al’adar ziyarar asibitin don duba marasa lafiya da ya gada iyaye da kakanni yayin da takwarorinsu masu lafiya ke gudanar da shagulgula a gidajensu.

Da yake mayar da jawabi, Sarkin ya yi alkawarin daukaka maganar zuwa ga hukumomin da abin ya shafa, inda ya yi addu’ar ci gaba da samun zaman lafiya a masarautarsa da Karamar Hukumar Jama’a da Jihar Kaduna da kuma kasa baki daya.

Bayan kammala ziyarar ce Sarkin ya koma fadarsa tare da ayarinsa a kan doki cikin ruwan sama mai karfin gaske, abin da ya takaita shagulgulan da aka shirya gabatarwa ga manyan baki da suka hada da Shugaban Karamar Hukumar Jama’a, Mista Peter Aberik da Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Hajiya Hadiza Sabuwa Balarabe sai dai duk da haka, ’yan rawar gargajiya na kabilun Numana da Koro daga kananan hukumomin Sanga da Kagarko da ’yan busar algaita sun yi wasa a cikin ruwan.