✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A gabana ’yan Boko Haram suka sace ’yar agaji abokiyar aikinmu – Shankat

A ranar 22 ga watan jiya ne ’yan kungiyar Boko Haram suka sace masu aikin jinkai a Jihar Borno, ciki har da wata jami’ar kiwon…

A ranar 22 ga watan jiya ne ’yan kungiyar Boko Haram suka sace masu aikin jinkai a Jihar Borno, ciki har da wata jami’ar kiwon lafiya ’yar asalin Jihar Filato, mai suna Jenepher Samuel Ukambong da take aikin tallafa wa jama’a kan kiwon lafiya a garin Manguno. Kan haka ne wakilinmu ya tafi kauyen Gura Topp da ke kusa da garin Bukur a Karamar Hukumar Jos ta Kudu da ke Jihar Filato, inda ya tattauna da abokin aikinta, mai suna Best Rebetmun Shankat, wanda al’amarin ya faru a kan idonsa. Kuma ya gana da mahaifiyar jami’ar kiwon lafiyar, mai suna Na’omi Samuel:

Mece ce dangantakarka da Jenepher Samuel, wacce ’yan Boko Haram suka sace?

Best Shankat: Abokiyar aikina ce, domin muna aiki a waje daya ne kuma mun gama makaranta daya ce. Ita kamar ’yar uwata ce kuma muna aikin asibiti ne a garin Manguno. Ni ma’aikacin jinya ne, ita kuma ma’aikaciyar jinya da ungozoma ce. Don haka muna wannan aiki ne a can, karkashin wata kungiyar kasa da kasa da take tallafa wa ’yan gudun hijira kan harkokin kiwon lafiya, mai suna Alliance for International Medical Action (ALIMA), wadda kungiyar jinkai ce a wannan a gari na Manguno. A wani asibiti ne a garin kungiyar take gudanar da aiki. Kuma a wannan asibiti akwai wurin haihuwa da kula da lafiyar yara. Kuma mun kai shekara biyu muna gudanar da wannan aiki a can

Mene ne ainihin abin da ya faru  lokacin da ’yan Boko Haram suka tafi da Jennifer?

A ranar Lahadi 22 ga Disamban bara, mun taso daga garin Manguno za mu tafi Maiduguri da misalin karfe 8 na safe, muna cikin tafiya a mota sai muka ga wata mota an bude gabanta. Muna tunanin ko sun samu matsala ce, mun zo daidai wannan mota sai muka ga wadansu mutum hudu sun fito rike da bindigogi; suka ce mu yi fakin. Direbanmu ya yi fakin, suka ce duk mazan da suke cikin motar su fito.

Kuma a lokacin da muka iso wajen, mun tarar da motoci kusan 20  da suka taso daga Manguno.  Suka zo suna tambayarmu mu kawo katin shaidarmu, suka fara bincikarmu.  A cikin motar da muka shiga akwai wani dan sanda mai mukamin Sufeto, suka tambaye shi katin shaidarsa. Sai ya ce ba ya da shi. Suka sanya hannu a aljihunsa suka fito da wata takarda da take dauke da wasu magunguna a ciki, sai suka fitar da shi daga cikinmu.

Sai suka dawo suka ci gaba da tambayarmu, ina katin shaidarmu, na ce masu ba ni da shi, suka bincike ni, ba su same ni da shi ba. Domin a lokacin da suke cewa mu sauka daga motarmu, sai na cire wallet dina daga aljihu, wanda ke dauke da katin shaidata da sauran takardu na boye a cikin motar.

Da suka gama caje mu sai suka tafi wajen motarmu, a cikin motar akwai mata uku da ita Jenepher Samuel. Sai suka ce mata ta sauka daga cikin motar, ta bi su. Daga nan sai suka dawo suka ci gaba da binciken motarmu. Da ma ita Jenepher Samuel wallet dinta yana hannuna a lokacin, don haka na boye shi a bayan inda muke zaune a cikin motar. Da suka dawo suka binciki cikin motar sai suka ga wallet dinta da ke dauke da katinta na dan kasa da katin zabe da lasisin tukin mota, suka tafi da shi.

Bayan kamar minti 20, sai suka fitar da wadansu mutane suka harbe su a gabanmu. Daga nan suka tara mu a waje daya, suka yi ta yi mana bayani da wani harshe, wanda ban gane harshen ba. Da suka gama bayaninsu sai suka ce, mu shiga cikin motocinmu mu tafi.

Gaskiya yadda na rayu a wannan al’amari, ikon Allah ne kawai. Ba wani wayona ko ilimina ba. Domin lokacin da wannan al’amari ya faru a gabana a nan suka tafi da wadansu mutane, bayan sun kashe wadansu.

Kamar mutane nawa suka bindige kuma mutane nawa suka tafi da su daga motarku?

A cikin motarmu sun tafi da Jenepher Samuel da wannan Sufeto dan sanda da na yi bayani a baya. Bayan haka akwai mutum biyu da suka tafi da su da suke cikin motar da take bayanmu. Haka na ga wadansu mutum biyu a bayan motarsu. A takaice dai mutum shida suka tafi da su, sannan mutum hudu suka kashe a gabanmu.

Yaya aka yi ka kubuta?

To, kamar yadda na fada, bayan da suka gama abin da suke so su yi, na kashe mutanen da suke so su kashe, sai suka ce mu shiga motocinmu mu tafi. Daga nan muka shiga motormu, muka koma Manguno, muka kai wa ’yan sanda rahoton abin da ya faru. Daga nan muka dawo muka kama hanyar zuwa Maiduguri. Da muka zo wajen da abin ya faru sai muka samu sojoji a wajen suna bincike.

A matsayinka na wanda kake tare da ita, me ka sani game da halayenta?

Gaskiya Jenepher Samuel daban take, halayenta masu kyau ne. Kuma tana aiki tsakani da Allah da zuciya daya. Don haka manya da yara, maza da mata kowa ke sonta a wajen da muke gudanar da aiki.

Lokacin da wannan abu ya faru, yaya ka ji a zuciyarka?

Gaskiya a lokacin na ji kamar duniya ta zo karshe ne. Don haka har yanzu ina cikin tsoro kan abin da na gani da idona, na kashe wadannan mutane da tafiya da wadansu. Tun daga faruwar wannan al’amari har zuwa wannan lokaci ba na jin dadin rayuwata. Domin wannan abu yana da muni. Haka muka zo aka yi bukukuwan Kirsimeti muna cikin bakin ciki. Kuma yadda nake ji yanzu, ina yi wa Allah godiya da karfin da yake bai wa mahaifiyarta da ’yan uwanta da ni kaina. Don haka muna jira mu ga yadda Allah zai yi ikonSa a kan wannan al’amari.

Daga faruwar wannan lamari zuwa yanzu, ko kungiyar da kuke yi wa aiki ta tuntube ku?

Sun yi magana da mu kuma sun tabbatar mana cewa suna kokarin ganin an kubutar da wannan jami’a.

Wane kira kake da shi ga gwamnati game da sace Jenepher Samuel?

Gaskiya a wannan kasa mun san matsalar da muke fuskata ta tsaro. Don haka ina kira ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Babban Hafsan Tsaro na Kasa da dukkan sauran jami’an tsaro, su tashi su magance wannan matasala ta tsaro. Domin Allah Ya ba su jagoranci da karfi, don haka muna rokonsu su dauki matakai na ganin an kubutar da wannan jami’ar kiwon lafiya, wadda ta je wannan waje don tallafa wa jama’a amma aka sace, aka tafi da ita. Don Allah gwamnati ta yi wani abu kan wannan al’amari don ganin an kubutar da ita.

Allah zai kubutar da Jenepher daga Boko Haram – Mahaifiyarta

Na’omi Samuel, ita ce mahaifiyar Jenepher Samuel kuma ga yadda Aminiya ta tattauna da ita dangane da abin da ya faru da ’yar tata a hannun ’yan Boko Haram:

Mece ce dangantakarki da Jenepher Samuel da ’yan Boko haram suka sace?

Na’omi Samuel: Ita ce ’yata ta biyu kuma mahaifinta ya rasu shekara 20 da suka gabata, wato tun tana da shekara 6 ya rasu, domin yanzu shekarunta 26.

Mene ne tarihinta?

Ita dai ma’aikaciyar asibiti ce, ta yi makarantartar firamare, bayan ta gama ta yi makarantar sakandAre. Daga nan ta tafi makarantar koyon aikin ungozoma. Daga nan ta ce bari ta je ta taimaki kasa a Manguno da ke Jihar Barno. Saboda kowa aka ce ya je can ya yi aiki ba ya so. Don haka ta ce ita ta bayar da kanta, don haka ta ce bari ta je ta taimaki mutanen da suke can. Saboda  bai kamata a guje su ba kan abubuwan da suke faruwa a can. Kuma ta taimaki mutane da dama a wajen, don haka take da kyakkyawar dangantaka da mutanen wajen.

Yaya kika ji a zuciyarki kan faruwar wannan lamari?

Na yi imanin cewa tunda Jenepher Samuel marainiya ce, Allah zai kubutar da ita ta dawo gida. Don haka na mika wa Allah komai kan wannan lamari. Tun daga ranar da wannan abu ya faru na mika wa Allah komai, domin na yi imanin akwai Allah kuma na yi imanin zai yi ikonSa, kan wannan lamari. Domin Allah Ya ce duk abin da ya faru da kai ka bar maSa. Don haka na bar wa Allah komai kan wannan al’amari. Na yi imani Allah zai kubutar da ita tare da sauran wadanda aka sace.

Daga faruwar wannan lamari zuwa yanzu, ko wadannan mutane sun tuntube ku?

Ka san ’yan Boko Haram ba su yin magana da iyalan wadanda suka sace. Masu garkuwa da mutane ne suke yin magana da iyalan wadanda suka sace. Amma mu dai maganar mun mika komai ga Allah kuma muna fata zai biya mana bukatarmu, kan wannan lamari.

Daga bangaren gwamnati an tuntube ku?

Gwamnati ta yi magana, domin Gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ya turo Kwamishinan Kasa da Safiyo da kuma Shugaban Karamar Hukumar Jos ta Kudu da Dan Majalisar Wakilai na wannan mazaba da Dan Majalisar Jiha na wannan mazaba, duk sun zo sun jajanta mana kuma sun ba mu tabbacin cewa za su yi kokari, wajen ganin an kubutar da ita.

Ina fata Allah Ya bai wa gwamnati basira ta magance wannan matsala ta tsaro da take damun kasar nan. Shekaru da dama kullum muna ji kamar waka, game da magance matsalar tsaro a kasar nan. A kullum za ka ga wani abu na matsalar tsaro ya faru a wurare daban-daban a Najeriya. Amma a kullum ana gaya mana cewa komai yana tafiya daidai. Don haka ina kira ga gwamnati, ta tashi tsaye ta magance wannan matsala ta tsaro a kasar nan, domin babu abin da ya fi karfin gwamnati.