✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

A rage kwanakin da alhazan Najeriya suke yi a Saudiyya – Barista Auwal

Babban Sakataren Hukumar  Alhazai ta Jihar Filato, Barista Auwal Abdullahi ya bukaci a rage yawan kwanakin da alhazan Najeriya suke yi a Kasa Mai tsarki.…

Babban Sakataren Hukumar  Alhazai ta Jihar Filato, Barista Auwal Abdullahi ya bukaci a rage yawan kwanakin da alhazan Najeriya suke yi a Kasa Mai tsarki.

Barista Auwal Abdullahi ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da Aminiya a garin Jos na Jihar Filato.

Ya ce ya kamata a rage yawan kwanakin da alhazai suke yi a Kasa Mai tsarki, domin alhazai za su iya kammala aikin Hajji a cikin kwana 20. Don haka yana da kyau a rage kwanakin alhazan suke yi, domin yin hakan zai saukaka musu wasu wahalhalu da suke fuskanta.

Sakataren ya ce raguwar alhazan da aka samu bana daga Najeriya, dole ne haka ta kasance saboda yanayin yadda kudin kujerar ya kasance da kuma halin rashin kudin da ake ciki.

Ya ce amma shi aikin Hajji kira ne na Allah, domin za ka ga wani ba ya da ko kwabo amma sai Allah Ya kawo masa hanyar da zai tafi, haka kuma za ka ga wani yana da kudin amma bai samu tafiya ba.

Barista Auwal ya ce a bangaren alhazan Jihar Filato a bana, sun samu gagarumar nasara domin tun daga tashinsu daga gida, ba a bar mahajjaci ko daya ba a kasa, kamar yadda aka saba yi a shekarun baya.

“Bayan haka an samar wa alhazan gida a Madina a kusa da harami  kuma kowanne maniyyaci ya samu abincin safe da dare a kan kari. Kuma kowanne maniyyaci ya sauka da kayansa daga Kasa Mai tsarki. Sannan kuma maniyyaciya daya ce ta rasu a bana a cikin alhazan Jihar Filato,” inji shi.

Sakataren ya ce Gwamnatin Jihar Filato ta yi namijin kokari kan aikin Hajjin bana, domin Gwamna ya daukin nauyin kujerun aikin Hajji 350 a cikin kujeru  800 na jihar. Kuma a duk lokacin da aka je da wata bukata kan aikin Hajjin, Gwamna yana kokari ya biya wannan bukata.