✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa muka kafa kungiyar Buhari/Masari Hannu da Hannu – Hajiya Jari Bala

Hajiya Jari Bala Batsari na daga cikin gogaggun ’yan siyasa mata wadda kuma ta yi fice a harkokin kungiyoyi. A cikin hirarta da wakilin Aminiya,…

Hajiya Jari Bala Batsari na daga cikin gogaggun ’yan siyasa mata wadda kuma ta yi fice a harkokin kungiyoyi.

A cikin hirarta da wakilin Aminiya, ta bayyana dalilansu na kafa wata kungiya mai suna Buhari/Masari Hannu da Hannu wadda ke da manufofin wayar da kan jama’a kan abin da ya shafi siyasa da kuma kokarin dogaro da kai.

“Abin da ya sa muka kafa wannan kungiya shi ne duba da irin yadda talaka ya sa hannu ya dangwala wa Buhari da Masari kuri’arsa ya zabe su da kansa ba wani ya zabar masa ba ko ya tursasa shi zabensu ba, wanda hakan ya zamo abin tarihi ne ga dan Najeriya domin tunda ake siyasa a Najeriya ba a taba siyasar da talaka ya zabi wadanda za su shugabance su ba.”

Shugabar ta kara da cewa ba wai siyasa kadai suka tsaya ba, “Muna da sauran manufofin da suka hada da fadakarwa domin sake zaben shi Shugaba Buhari da shi Gwamna Masari a zabe mai zuwa. Sannan mun lura da irin yadda a kullum tarbiyar mata da matasa take kara tabarbarewa ta fuskar shaye-shaye, wannan ya sa mun sanya wannan cikin manufofinmu ta hanyar fadakarwa don kaurace wa wannan muguwar dabi’a da ta fara zama ruwan dare. Kuma mun sanya batun koyar da sana’o’i ga matasa.

Dalilin kawo wannan tsari kuwa shi ne duk abin da kake so mutun ya yi, in bashi da abin da zai yi sai a taras duk wani abin da za ka nuna masa na dogaro da kai bai yi tasiri ba domin bai san yadda zai yi ya dogara da kansa ba.”

Shugabar kngiyar ta kara da cewa baya ga mayar da hankali a cikin karkara domin nan ne suke bukatar abubuwa, “Dalilin daukar wannan mataki shi ne matasa su koyi sana’a. To amma sai ya zamo mu muka koyar kuma muke zuwa mu saya, wannan zai kara bayar da kwarin gwiwa. Kuma duk kayan da muka saya, su ne za mu je kuma mu raba wa jama’a walau ta bayar da gudunmuwa ko kuma lokacin yakin neman zabe. Maimakon sabulai da man shafa ko takalman da za mu je wani wuri mu sawo mu raba. Kuma ina tabbatar maka da cewa har zuwa yau din nan ban iya cewa ga yawan kayan da jama’armu suka yi ko suka sayar,” inji shugabar.

Saidai kuma Shugabar ta ce babbar matsalar da suke fuskanta a yanzu ita ce ta rashin zuwa karbar katin zabe, “Ga mutun ya yi rajistar zabe, amma zuwa ya karba sai abin ya zama matsala. Hakan kuwa ba karamar illa ba ce musamman a bangaren Arewa. Sai batun yadda wasu ke yi wa koyon sana’a rikon sakainar kashi.

Sannan sai tayi kira ga masu hali da su rika taimaka wa kungiyoyi irin nata. “Ita kungiya ba ana yinta don siyasa kadai ba ce, akwai wurare da dama da take amfani. Saboda haka nake kira ga duk wani wanda ya ji zai iya to ya rika taimaka wa ko ta hanyar kawo mana kayan koyon sana’ar ko su zo su saya. Su kuma masu koyon sana’ar to su rike ta hannu biyu. Sannan kuma ga zaben 2019 nan na kara matsowa. Shugaba Buhari da Gwamna Masari na neman kuri’unku,” kamar yadda ta ce.