Da Dumi Dumi

Abin da yake hana ni fitowa a fim  – RashIda  Maisa’a

Rashida Adamu Maisa’a

Jakadiya Rashida Adamu Maisa’a fitacciyar jarumar fina-finan Hausa ce, kuma a yanzu take rike da mukamin Mai ba Gwamnan Kano Shawara a Kan Harkokin Mata. A hirarta da Aminiya ta bayyana dalilin da ya sanya aka daina ganinta a fim da kuma yadda ta tsinci kanta a harkar siyasa.

 

Wace ce Rashida Maisa’a?

Sunana Jakadiya Rasheedat Adamu Abdullahi wacce aka fi sani da Maisa’a. Ni ’yar Karamar Hukumar Tarauni ce a nan Jihar Kano. Na yi karatun firamare a Tarauni sai na wuce Jihar Jigawa na yi sakandaren mata ta Garki. Daga nan na wuce wata makaranta a kasar Sudan wato Ma’haj inda na yi karatun diploma, sannan na wuce wata jami’a a Kwatano a kasar Benin inda na yi digiri a fannin kimiyyar siyasa. Bayan na kammala sai na dawo na shiga harkar fim inda zan iya cewa na yi fina-finai da dama.

 

ADVERTISEMENT

Wane fim kika fara yi?

Fim dina na farko shi ne ‘Jariya’ wanda Abubakar Sani Mawaki ya yi. Daga nan sai na yi fim na biyu mai suna ‘Sa’a’.  Fim din Sa’a fim dina ne, ni ce da kudina na yi shi.  Daga nan kuma na ci gaba da yin fina-finai na kaina a karkashin kamfanina. Na fito a fina-finai da dama amma fitattu daga cikinsu su ne Tutar so, da Halwa na Ali Nuhu, da Gobe-Da-Nisa da sauransu.

 

Wane kalubale kika fuskanta lokacin da kike yin fim?

A gaskiya tun ina fitowa a fim har ta kai ina yin nawa na kaina har zuwa lokacin da na koma siyasa aka ba ni mukamin Mai ba Gwamna Shawara kan Harkokin Mata, ban taba samun wani babban kalubale ba. Don ina tabbatar maka babu wata kafa ta watsa labarai ko wata jarida da ta taba fadar wani aibina, illa dai wadansu da suke shigowa harkar suna fakewa da harkar fim suna bata sunan ainihin ’yan fim din, wannan shi ne kawai kalubalen.

 

Wa kika fi jin dadin aiki da shi a Kannywood?

Duk da yake na yi aiki da masu yin fim da dama amma Abubakar AS Maikwai shi ne wanda na fi jin dadin aiki da shi. Domin yana daya daga cikin wadanda suka daga darajata a duniyar fim.

 

Ina kika samo sunan Maisa’a?

Na samo wannan suna ne daga fim dina na Sa’a, kuma Allah ne Ya daga darajata a fim ta wannan fim din don haka shi ne fim din da na fi so a rayuwata.

 

Me ya sanya aka daina ganinki a cikin fim?

A gaskiya likafa ce ta ci gaba, ka ga tun ina fitowa cikin fim din wadansu har ta kai ina yin nawa na kaina a karkashin kamfanina har kuma yanzu na zo na shiga cikin harkar siyasa kuma Allah Ya yi min albarka aka ba ni mukamin Mai ba Gwamna Shawara kan Harkokin Mata. To ka ga wannan aikin nawa na ba Gwamna shawara aiki ne da yake bukatar zuwa ofis don haka ba ni da lokacin zuwa wajen daukar fim duk da yake ana kawo mini bukatar yin haka daga lokaci zuwa lokaci.

 

Ko haka na nufin kin bar Kannywood ke nan?

A’a, duk da yake a halin yanzu na fi karkata wajen siyasa amma har yanzu ina nan daram a ciki. Yanzu na zama uwa mai bada shawara. Sannan har yanzu ina da kamfanina na fim wanda a halin yanzu in dai za ka kidaya kamfanona uku masu kayan aiki a duniyar Kannywood, to, dole za ka sanya shi a ciki. Amma fim din da na yi na karshe shi ne fim din Ali Nuhu wato Mujadala.

 

Yaya aka yi kika tsinci kanki a siyasa?

Wannan wani abu ne da na fara kamar wasa ina dari-dari da shi. Amma cikin ikon Allah sai ga shi Allah Ya taimaka Mai girma Gwamnan Jihar Kano Dokta Abdullahi Ganduje ya ga irin gudunmawar da nake badawa kuma ya ga na cancanta ya ba ni mukamin Mai ba Gwamna Shawara kan Harkokin Mata.

 

Wadanne nasararori kika samu kawo yanzu a sabon mukamin naki?

A gaskiya na samu nasarori da yawa a karkashin jagorancin Khadumil Islam da kuma matarsa Mamanmu Dokta Hafsatu Umar Ganduje. Ka ga mun samar wa mata sana’o’i da ayyukan yi ta yadda za su dogara da kansu. Sannan akwai abubuwan da suka shafi kiwon lafiyarsu da sauransu.

 

Yaya yanayin shigar mata harkar siyasa?

A gaskiya ana samun ci gaba, domin ka san a da idan aka ga mace a siyasa sai a rika yi mata wani kallo. Amma yanzu ya zama abin sha’awa, a kullum ina samun mata da dama da kan zo ofis suna yaba mana tare da kokarin kawo shawara kan yadda mata za su shiga siyasa a dama da su. Kuma ni kaina na samu kyaututtuka na girmamawa da dama a kan wannan mukami da nake a nan cikin gida Najeriya da wasu kasashe. An karrama ni a Landan kuma a yanzu haka an gayyace ni zuwa kasar Kanada wanda zan je cikin wannan wata duk a kan harkokin mata.

 

Na ji ana kiranki Ambasada wato Jakadiya daga ina kika samo wannan mukami na Jakadiya?

Da farko dai na samu Ambasadar Matasa ta Jihar Kano daga Jami’ar Tarayya ta Dutse, a Jihar Jigawa sannan aka ba ni Jakadiyar ’Yan fim ta Arewacin Najeriya daga Masarautar Zazzau. Sannan aka ba ni Garkuwar ’Yan fim daga Masarautar Neja. Daga kasashen waje kuma na samu Jakadiyar Zaman Lafiya ta Arewa daga wata kungiya mai zaman kanta wato NASMA wacce take a birnin Landan.

 

Wane sako gare ki ga matasa masu sana’ar fim musamman mata?

Sakona gare su shi ne su dage su yi sana’ar nan da gaskiya. Su kare mutuncin kansu da na gidajen da suka fito ta hanyar kauce wa yin duk wani abu da ka iya bata sunansu.

 

Wane sako gare ki ga masoyanki?

Duk da yake ba na fitowa a cikin fim a halin yanzu saboda ayyukan ofis amma dai ina nan tare da masoyana kuma ina yi musu godiya kan irin soyayyar da suke nuna mini.

 

 

 

Share