Da Dumi Dumi

Abubuwa uku da ke hallakar da matasa (2)

Abubuwa uku da ke hallakar da matasa (2)

2-Kallace-Kallace;

Ta wadannan kafafe ne matasanmu ke daukar wasu bakin  dabi’u, kama daga aski, sanya wando ko rika, sanya sarka a wuya, sanya ’yan kunne, sanya katon tabarau da sauransu.

A yanzu wadansu iyaye sun dauki wadannan kafafe a matsayin abokan hira, ni kuma na kira su abokan shashanci. Daga lokacin da matashi ya siffantu da kamanni na wadansu mutane sannu a hankali sai ka ga dabi’unsa sun rikide sun koma irin nasu.

Wadansu malaman tarbiyya sun ce: Ko makiyayi ne da ke yawan cudanya da dabbobi, hakika zai dauki halaye irin na wadannan halittu da yake damfare da su a kowane lokaci.

A nan zan yi kira ga iyaye wadanda kai-tsaye suke da hakkin kula da tarbiyyar ’ya’yansu da kada su sakar musu tashoshi, musamman na batsa da kade-kade da  fina-finai na Hausa da na  Turawa ko Amurkawa da sauransu.

ADVERTISEMENT

Haka kuma kada su bar su da wayoyin hannu, Kamar yadda na sha fada a baya sai ka ga yarinya ’yar shekara 12 tana rike da manyan wayoyi da hankali ba zai dauki irin ta’asar da sukan iya janyowa ba.

Hausawa sun ce gyara kayanka bai zamo sauke mu raba ba.

3-Shaye-shaye

Annabi (SAW) ya ce “Duk abin da ke sa yin maye  giya ne, kuma kowace giya haramun ce.” Kamar yadda na ambata a sama, ita barna matakai gare ta, idan aka rasa aikin yi ga mafiya yawan matasanmu, sai su buge da kallace- kallace, daga nan sai aron al’adu sai shaye-shaye, an ce daga inda tururuwa ta yi fuka-fuki to lalacewarta ya zo. To haka yake ga matashin da ya riki kayan maye, wata rana sai ka ji shi yana yin dauke-dauken abin da bai ajiye ba.

A nan zan yi kira ga hukuma wanda hakkinta ne kula da kare hankalin jama’a, kuma akwai wasu gwamnatocin da ke kamawa da kona kayan maye wannan abu ne mai kyau.

Allah Ya shiryar da mu da zuriyar da Ya ba mu, Ya gafarta mana kura-kuranmu kuma Ya sa mu cika da imani, amin summa amin.

Sanusi Hashim Abban Sultana

Jihar Katsina

08065507271

Share