Search
Subscribe
Aisha Buhari ta nemi afuwar iyalanta da ‘yan Najeriya

Aisha Buhari ta nemi afuwar iyalanta da ‘yan Najeriya

Uwargidan shugaban Najeriya Hajiya Aisha Muhammadu Buhari ta nemi afuwar ‘ya’yanta da iyalanta da kuma daukacin ‘yan Najeriya kan bidiyon da aka gan ta tana fada a cikin daki, wanda aka yi ta yada shi a makon da ya gabata.

A cikin wannan bidiyon dai an ji Aisha Buharin tana ta fada a harshen Turanci, duk da dai ba a nuna fuskarta ba da mai daukar hoton bidiyon.

Ranar Aisha da ta dawo daga Ingila ta tabbatarwa manema labarai da cewa ita ce a bidiyon amma diyar Mamman Daura Fatima ce ta dauke ta. Fatiman dai ba ta musanta ba a lokacin da BBC ta tuntube ta.

Kazalika Aisha Buharin ta mika godiyarta zuwa ga maigidanta shugaban Najeriya kan sabbin mukamai shida da ya yi wa ofishinta na masu taimaka mata na musamman.

Hakan na cikin sanarwar da mai taimaka mata kan harkokin yada labarai Suleiman Haruna ya fitar a ranar Larabar. Mataimakan sun hada da:

Dr. Mairo Almakura – Mai taimaka mata ta musamman kan Kungiyar Matan Shugabannin Kasashen Afirka AFLPM.

Muhammed Albishir – Mai taimaka mata ta musamman kan Kungiyar Matan Shugabannin Kasashen Afirka kan Ci gaba OAFLAD.

Wole Aboderin – Mai taimaka mata na musamman kan Kungiyoyi Masu Zaman Kansu NGOs

Barista Aliyu Abdullah – Mai taimaka mata na musamman kan Harkokin Yada Labarai

Zainab Kazeem – Mai taimaka mata ta musamman kan Harkokin Cikin Gida da Tarukan Nishadi

Funke Adesiyan – Mai mataimaka mata kan Harkokin Cikin Gida da Tarukan Nishadi.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin