Wani rahoto daga kasar Sudan ya bayyana cewa kimanin mutum 11 ne suka mutu a wata zanga-zangar neman maida kasar a kan tafarkin mulkin farar hula.
’Yan sanda sun harba barkonon tsohuwa a kan dubban masu zanga-zang a ranar Lahadin da ta gabata a Birnin Khartoum, da wasu sassan kasar.
Da take tofa albarkacin bakinta game da kisan da aka yi ga masu zanga-zangar, Gwamnatin Amurka ta yi Allah wadai da irin karfin da aka nuna a kan masu zanga-zangar.
A halin yanzu kuma, yayin da masu zanga-zangar ke ci gaba da matsa lamba a kan sojojin da suka tumbuke tsohon Shugaban Kasar Sudan Omar al-Bashir, su hanzarta maida kasar a kan tafarkin dimokuradiyya, akwai alamar cewa kungiyoyin kishin Musulunci suna fuskantar kalubale wajen samun bakin magana a kan makomar kasar kamar yadda Muryar Amurka ta ruwaito.
Wadannan kungiyoyin na ’yan kishin Musulunci sun taka muhimmiyar rawa wajen taimaka wa al-Bashir ya dare kan karagar mulki.
Wannan ya sa ake ganin halin da aka shiga yanzu a Sudan ba zai taimake su samun shiga a cikin kungiyoyin da ke sahun gaba wajen shata sabuwar makomar kasar ba.