✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar a sulhunta Hadiza Gabon da Amina Amal

A wani bincike da Aminiya ta yi ta gano akwai yiwuwar a sasanta jaruma Hadiza Gabon da kuma Amina Muhammad wadda aka fi sani da…

A wani bincike da Aminiya ta yi ta gano akwai yiwuwar a sasanta jaruma Hadiza Gabon da kuma Amina Muhammad wadda aka fi sani da Amina Amal bayan rikicin da ya barke a tsakaninsu a makon jiya.

Wata majiya ta bayyana wa Aminiya a yanzu haka ana zama tsakanin lauyoyin Amina Amal da kuma shugabannin ’yan fim a karkashin Motion Pictures Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN) da kuma Arewa Filmmakers Association of Nigeria (AFMAN).

Aminiya ta fahimci ana wannan zaman ne a Kano, kuma ajandar da zaman ita ce yadda za a sasanta jaruman ba tare da an je kotu ba.

Idan ba a manta ba dai a kwanakin nan masana’antar fina-finan Hausa da ake kira Kannywood ta samu kanta rudani dalilin dora wani hoton tsiraici da jaruma Amina Muhammad wadda aka fi sani da Amina Amal ta yi a shafin sada zumunta na Instagram.

A hoton jarumar ta sanya matsattsun tufafin da suka fitar da surarta har da cibiyarta a waje, hakan ya sanya mutane suka yi alla-wadai da abin da ta yi, inda a ciki har da ’yan fim da suka hada da Hadiza Gabon da A’isha Aliyu Tsamiya da Hassan Giggs da Baballe Hayatu da sauransu.

A karkashin hoton da Amal ta sanya din ne Gabon ta rubuta ba da haka Amal za ta yi suna ba, inda A’isha Tsamiya ta ce abin da Amal ta yi ne yake sa a rika zagin Kannywood.

Sai dai bayan kwana daya sai Amina Amal ta sake sanya wani hoto a shafinta na Instagram mai dauke da wata hira, inda a karkashin hoton ta rubuta sai dai a kira ta karuwa saboda shigar tsiraici da ta yi, amma ita ba ta madigo.

Wannan al’amari ne ya sanya aka fara zargin ko da Gabon take, inda aka wayi gari wani bidiyo mai tsawon minti 1 da sakan 30 yana yawo a kafar sada zumunta.

A bidiyon wanda aka dauka a juye an ga jaruma Amal zaune a kan katifa, inda wata murya da ake zargin ta Hadiza Gabon ce take umartar Amal ta karanta sakonnin da suka tura wa juna ta Instagram, inda hakan ya kai har da mari da duka.

Sai dai a bidiyon wani da aka kira Ustaz ya kira jaruma Gabon da Ustaziya, inda ya bukaci ta daina dukan Amal. A bidiyon ta Gabon ta yi addu’ar idan har ta cuci Amal to Allah Ya hana ta abin da take so duniya da lahira.

Bayan haka ne wani bidiyo mai dauke da minti 1 da sakan 30 ya sake fita, a bidiyon an nuna Amal a wani shago, sannan jaruma Gabon tana yi mata tambayoyi. Gabon ta tambayi Amal ko ta taba nemanta da iskanci ko ta taba cutar da ita, inda Amal ta amsa da a’a.

Amal ta bayyana cewa sharrin shaidan da kuma shaye-shaye ne ya sanya ta yi wa Gabon hakan, inda dalilin neman kare kai da Gabon ta yi ne ta fitar da wadansu bayanai na hirarraki tsakaninta da Amal, inda a nan aka gano yadda Amal take neman taimakon kudi a wurin Gabon saboda matsalar rashin lafiyarta ko ta mahaifiyarta.

A cikin bayanan da Gabon din ta fitar ne ma aka gano yadda Amal take cusa kanta a wurin Gabon, inda idan har Amal ta yi wa Gabon magana a Instagram ba ta amsa ba sai ta shiga damuwa.

Sai dai duk da wadannan bayanai jama’a sun ci gaba da cece-kuce a kai, har wadansu suka bayyana ai Amal ba ta ma ambaci sunan Gabon a cikin bayaninta na zargin madigo da ta fitar a shafinta na Instagram ba.

Al’amarin ya kara dagulewa ne bayan da lauyoyi 12 suka nemi kwato wa Amal hakkinta na cin zarafinta da suke zargin Gabon ta yi.

Sai dai ana cikin hakan ne sai jaridar Leadership A Yau ta ranar Asabar 13 ga Afrilu, 2019 suka fitar da labari mai taken “Amina Amal Ta Kwanta Jinya Bayan Dukan Da Hadiza Gabon Ta Yi Mata”.

Jaridar Leadership A Yau ta rawaito cewa a yanzu haka Amal tana fama da yanayi na rashin lafiya da kuma rudewa sakamakon mumman tashin hankalin da ta fuskanta tun a daren farko da jaruma Gabon da tawagarta suka far mata a gidanta da ke Kaduna.

Jaridar ta ce, majiyar da ta yi magana da ita ta ce ana zargin har sai da (’yan tawagar Gabon) suka danne ta (Amal) suka dura mata kayan maye, don ta fadi abin da su ke son ta furta a bidiyon da Gabon din ta dauke ta lokacin dukan.

Jaridar ta kara da cewa a yanzu Amal ta bar Kaduna, saboda hadarin da rayuwarta ke ciki bisa hasashen za a iya daukar nauyin ’yan ta’adda su sake kai mata hari.

Jaridar ta rawaito jim kadan bayan Amal ta bar Kaduna a yanzu ta kwanta jinya sakamakon barazanar da ta fuskanta, inda yanzu haka likitoci na kokarin ceto rayuwarta ne saboda ana kyautata zaton cewa lamarin ya haifar mata da ciwo a zuciyarta.

Labarin na Leadership A Yau bai yi wa wata kungiya mai goyon bayan jaruma Gabon dadi ba, inda suka zargi jaridar da kara rura wutar rikici tsakanin gwanarsu da kuma Amina Amal.

Kungiyar mai suna Team Adizatou Gabon cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabarta, Farida Mafara, ta yi zargin cewa labarin da jaridar ta fitar a ranar 13 ga Afrilu, 2019 mai taken “Amina Amal Ta Kwanta Jinya Bayan Dukan Da Hadiza Gabon Ta Yi Ma Ta” ba gaskiya ba ne, an kuma rubuta shi ne don wata mummunar manufa.

Kungiyar ta ce a labarin an rubuta Amina Amal ta kwanta jinya, amma a labarin babu sunan asibitin da ta kwanta jinyar, ba a bayyana ko a gida ta kwanta jinyar ba, an kuma ce jarumar ta bar gari don gudun kada a kai mata farmaki.

Ta kara da cewa hakan ya nuna an yi tufka da warwara a labarin, saboda an ce jarumar ta kwanta jinya, kuma an ce ta gudu. Ta yaya wanda ke kwance jinya zai gudu? Sai dai ko a gudu da shi ko?

“Bincikenmu ya nuna Amal ba ta kwanta rashin lafiya ba, hasalima tana wani otal da ke Kano tana shakatawa abinta. Sannan kuma a-kai-a-kai tana ta dora hotuna a shafinta na Instagram, wanda ke kara shaida lafiyarta kalau” Inji Farida.

Kungiyar ta zargi cewa jaridar ta rubuta labarin ne saboda jaruma Gabon ta taba samun sabani da editan jaridar, inda a yanzu yake ganin lokaci ne da zai yi amfani da damarsa wajen bakanta wa gwanarsu.

“Abin da ya faru shi ne a shekarun baya, editan jaridar ya taba samun Hadiza Gabon ya ce su hada kudi su yi fim, inda ta ba shi Naira miliyan 2 da dubu 800, an yi fim din amma bai dawo mata da kudinta ba,

“Jarumar ta kai kararsa (Gwangwazo) gaban kungiyar ’yan fim ta MOPPAN, inda aka zauna, a karshe ya ba ta Naira miliyan 2 da kyar, inda ta yafe masa sauran Naira dubu 800, amma duk da haka daga lokacin ya kullaci jarumar, yanzu kuma yake ganin ya samu damar bakanta mata.” Inji Farida.

Farida ta kara da cewa a yanzu haka abin yana damun jaruma Hadiza Gabon, tana jin inama wannan hargitsi ba a yi shi ba. Kuma ya kamata a yi mata uzuri saboda dan Adam tara yake bai cika goma ba.

Ta ce, “Fatanmu shi ne a sasanta ta hanyar da ya fi alkhairi ga masana’antar, don haka muna kira ga jaridar Leadership A Yau ta kasance jakadiyar zaman lafiya ba jakadiyar kara rura wutar rikici ba.”

Sai dai Aminiya ta tuntubi Editan Jaridar Leadership A Yau, Nasir S. Gwangwazo inda ya ce ba shi da hannu wajen rubuta labarin.

Ya ce, “Ni editan jaridar ne daga Litinin zuwa Juma’a, ba ni da iko a kan labaran da za su fita ranar Asabar da Lahadi, don haka ba ni da hannu wajen rubuta labarin.

“Tabbas na yi huldar kasuwanci da Gabon amma ban kullace ta ba, babu kuma wata riba da zan ci a kan labarin da aka buga a Leadership domin ban ma taba ganin Amina Amal ba, ballantana a ce ina goyon bayanta.” Inji shi.

Ya ce, idan ma abin da aka zarge shi na kasa biyan Gabon ragowar Naira dubu 800 gaskiya ne, sannan har kuma ta yafe masa kudin da take binsa, kamata ya yi ya zama dan gidanta, ba wanda zai kullace ta ba.

Aminiya ta kira Amina Amal ta waya sau 12, ta tura mata sako kan batun ko ta kwanta jinya dalilin dukan da ake zargi an yi mata, amma jarumar ba ta amsa waya ba, ba ta kuma ba da amsar sakon da aka tura mata ba.

Da aka tuntubi jaruma Gabon ko ta sa an yi wa Amal dukan kawo wuka har ta kwanta jinya, sai ta ce a tuntubi Manajanta kuma mai magana da yawunta, wato Ibrahim Birniwa.

Birniwa ya ce abubuwan da aka rubuta a labarin kirkirarru ne, “an fake ne a karkashin damar da aka bai dan jarida ta boye majiyarsa aka yi mugayen bayanan da babu su.”

Ya ce, mafi muni shi ne inda aka ce wai Hadiza ta yi hayar ’yan ta’adda domin su kashe Amal, ai ka ga wannan daga ji zance ne marar tushe, kuma ko a cikin Kannywood din mutane suna ta Alla-wadai da wannan rubutu da aka yi mai cike da kiyayya.

Ya ce, “A labarin Leadership ba su tuntubi bangaren Hadiza Gabon domin yin ‘balancing’ labarinsu ba, wanda dole haka ya kamata a yi a bisa tsarin aikin jarida, sannan ba a ji kuma a cikin rubutun an ce an yi kokarin tuntubar bangaren Hadiza din ba. To ka ga wannan kawai wani yunkuri ne na shafa wa Hadiza kashin kaji da nufin jawo mata tsana daga jama’a.”

Ya ce idan har labarin da jaridar ta rubuta gaskiya ne to ya kamata duk inda aka ga Gabon ma a jefe ta, “to Alhamdulillahi mutane sun sani Hadiza mace ce mai kirki ba za ta taba yin tunanin sa a kashe wani ba.” Inji Birniwa.