✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’irshadiyya ta yaye dalibai matan aure karon farko cikin shekaru 12 a Legas

A jiya Lahadi ne makarantar Al’irshadiyya ta yi walimar yaye dalibai matan aure guda 9 da suka sauke karatun al’kur’ani mai girma a unguwar mil…

A jiya Lahadi ne makarantar Al’irshadiyya ta yi walimar yaye dalibai matan aure guda 9 da suka sauke karatun al’kur’ani mai girma a unguwar mil 12 da ke Legas karo na farko cikin shekaru 12 da kafuwar makarantar.

Malama Maryam Dayyabu, ita ce shugabar makarantar ta shaidawa Aminiya cewa, makarantar ita ce, irin ta ta farko a yankin wacce mace ce ke koyar da ‘yan uwanta mata, “Na yi gwagwarmaya kwarai kafin na kai ga kafa wannan makarantar, na jajur ce ne duba da mahimmancin ilimim mata tare da raunin su da sakacin ta fuskar neman ilimi, wannan dalilai ne suka sanya na dage har Allah ya taimake mu muka kai ga kafa wannan makaranta” Ta ce, duk da akwai makarantun matan aure da dama a yankin amma maza ne ke koyar da matan auren kuma ba duk namiji bane ke lamuntar hakan ba, kuma damar ciwon mace na ‘ya mace ne, idan mace ce take koyar da ‘yar uwar ta mace za a fi samun daidai to domin za a sami ikon fayyace komai ba tare da matsalar kunya ko wani abu makamancin haka ba.

 

Ta ce, dalibai matan da aka yaye za su ci gaba da tallafa wa mata wajen koyar da matan auren, kana suna da muradin gina makaranta mai zaman kanta a maimakon gidan da suke amfani da shi wanda yake a matse, “Da dalibai 5 zuwa 7 na kafa makarantar amma yanzu muna da dalibai 70 zuwa 80 don haka burin mu shi ne mallakar makarantar matan aure ginanna mai zaman kanta a unguwar Mil 12 a Legas”.