✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Almajiranci a Zariya: ‘Tashin hankali a yankinmu na Katsina na hana mu zuwa duba iyayenmu’

Garin Zariya na daya daga cikin garuruwan da ake samun tururuwar kananan yara da ake turowa daga wasu garuruwa da kauyuka da sunan karatun allo,…

Garin Zariya na daya daga cikin garuruwan da ake samun tururuwar kananan yara da ake turowa daga wasu garuruwa da kauyuka da sunan karatun allo, inda almajiran suke fama da yawon barace-barace duk da ce garin na daya daga cikin wuraren da aka bude makarantun allo na zamani.

Wani almajiri mai suna Buhari Ibrahim wanda ya fito daga Nasarawar Faskari ta Jihar Katsina kuma yake almajiranci a makarantar Malam Umaru da ke bayan firamaren Tudun Jukun ya ce, “Mu biyar aka kawo mu da kanena mai suna  Kabiru Ibrahim da Nazifi da Bello sai Anas. Dukanmu ’yan gari daya ne kuma yanzu shekararmu 4 da zuwa. Ba mu da wata damuwa kuma malaminmu ya ce duk mai son shiga makarantar boko yana iya shiga tunda makarantar tana kusa da mu, sai dai ba wanda ya shiga kuma wadansu daga cikinmu suna da gidajen da suke aiki kuma masu gidajen suna kula da su har ma kayan sawa suna yi musu da Sallah kuma suna kula da lafiyarmu,” inji shi.

Ya ce “Kuma abin da ya kara karfafa zamanmu a makaranta shi ne yadda wurarenmu suka zama ba kwanciyar hakali saboda yadda ake satar mutane da dabbobi da kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Wannan ya sa mu zama a nan domin mu yi karatu mun fi samun kwanciyar hankali.”

Buhari ya ce, sukan shiga damuwa idan suka tuna da iyayensu, kuma idan daya daga cikinsu ba ya da lafiya to sai dai su da kansu su kula da shi ko inda suke aiki su dauki dawainiyar kula da su idan suna fama da rashin lafiya. “Kuma duk shekara bayan kammala aikin gona an kintsa amfanin, malaminmu yana zuwa kauyenmu domin karbo abinci daga wurin iyayenmu domin idan muka je bara ba mu samo ba to sai mu aika cikin gidan malam mu karbo abinci. Haka muke rayuwa har ma wadansu daga cikinmu sun fara saukar Alkur’ani,” inji shi.

Sai dai ya ce tunda suka zo Zariya ba su taba zuwa gida ba saboda garin nasu suna cikin fargaba ko sun ce za su je sai a ce kada su zo domin gari ba lafiya sai dai wani lokaci wani daga cikin iyayensu ya zo.

Aminiya ta ziyarci tsangayar wani malami da ke garin Shika a Karamar Hukumar Giwa, mai suna Malam Abubakar Dauda  wanda aka fi sani da Alaramma ko Abubakar Mai Almajirai, Hayin Katsinawa, wanda ya ce ya kai kusan shekara 30 yana karantar da almajirai kuma yanzu haka yana da ressan tsangaya 35 da ya koyar da su suka je suka bude nasu makarantar allon a wurare daban daban a jihohin kasar nan.

Alaramma Abubakar ya ce, yana ganin kuskuren gwamnati ta yadda idan ta tashi tsara wani al’amari da ya shafi almajirai ba ta neman wadanda suka san harkar koyarwa a tsangaya su ba ta shawarar da ta kamata a bi, don a  samu nasara. “Ka ga kamar ni na san yadda kasar Sudan ta samar da nata makarantun tsangaya na zamani wato makarantun allo irin namu, da yadda take tallafa wa makarantu har ma wadannda ba su da galih suna zuwa irin wadannan wurare suna samun tarbiyya. Don haka ka ga ba su da almajirai masu yawace-yawace irin namu suna da tsari mai kyau wanda yake amfanar da al’umma ba tare da matsala ba,” inji shi.

Alaramma Abubakar ya ce in da gaske gwamnati take yi sai ta nemo wadanda suka san tsarin ko suka dade a cikin harkar koyar da almajirai su ba su shawara domin a samu nasara, “Mu da muke kokarin karantar da yara ai taimakon gwamnati muke yi domin galiban yaran da ake kawowa almajiranci yanzu kusan duk wurarensu ba su da kwanciyar hankali don haka babu abin da ya dace su yi illa su turo yaransu almajiranci ko sa samu kwanciyar hankali,” inji shi.

Ya ce, suna maraba da matakin da gwamnati ke dauka na hana bara, domin ba wai suna karantar da su kawai ba ne suna koya musu sana’a da noma da kiwo da dinki da sauran sana’o’i.

“Gwamnati ta shigo ta ga yadda muke yi ta sa hannu wajen daukar nauyin koyar da sana’o’i, idan ta yi haka za su ji dadi “Domin bara da kake gani ba ma so ko kadan domin kaskanci ne kuma galibin yaran da ake kawowa wadansu iyayensu marasa galihu ne ba su da abinda za su biya wa yaran kudin makaranta. Ka ga dole su kawo su irin wannan don gudun kada yaro ya lalace,” inji shi.

Da Aminiya ta ziyarci makarantar tsangaya ta musamman da Gwamnatin Tarayya ta gina domin almajirai mai suna Umaru Musa ’Yar’aduwa Almajirai Lingual (Model Boarding) da ke Marabar Gwanda a hanyar Kano ta tarar da makarantar a rufe.

Wani makwabcin makarantar wanda dansa ke karatu a wurin mai suna Malam Jabiru ya ce tunda aka ba da hutu yaransu ba su koma ba, da suka nemi jin dalili sai aka sanar da su cewa babu abincin da za a bai wa dalibai ne a makarantar, don haka ya sa ba a koma ba.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin shugaban makarantar Malam Abdulhamid, inda ya shaida mata ta waya cewa ba zai yi magana ba, sai ya samu izini daga Ma’aikatar Ilimi ta Jihar Kaduna wadda yake karbar umarni daga gare ta.

Amma ya amince cewa abin da ya hana daliban dawowa makarantar shi ne ba su riga sun samu abin da daliban za su ci daga hannun gwamnati ba, tunda daliban kusan 300 ne da suka fito daga Kananan hukumomi 23 na Jihar Kaduna.

“Ka ga kuwa ba za ka rabo dalibi daga gidajen iyayensu ba, ba tare da ka ba su duk abin da suke bukata ba, don haka ya sa ba a komo ba,” inji shi.