✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Al’ummar Tafawa balewa sun fara yunkurin janye dan majalisarsu na Tarayya

Al’ummar karamar Hukumar Tafawa balewa da ke Jihar Bauchi su fara yunkurin janyen dan majalisa mai wakiltar mazabar Tafawa Balewa da bogoro da Dass, Barista…

Al’ummar karamar Hukumar Tafawa balewa da ke Jihar Bauchi su fara yunkurin janyen dan majalisa mai wakiltar mazabar Tafawa Balewa da bogoro da Dass, Barista Yakubu Dogara, saboda ya gabatar da kudiri a gaban Majalisar Tarayya yana neman a sake mayar da hedkwatar karamar hukumar zuwa Tafawa balewa daga Bununu ba tare da la’akari da rashin zaman lafiya da aka yi fama da shi a yankin ba.
Dukkan sarakuna da jami’an gwamnati na karamar hukumar ne suka je Majalisar Dokokin Jihar Bauchi don gabatar da takardarsu domin mika ta ga Shugaban Majalisar Tarayya, sannan suka wuce Cibiyar ’Yan Jarida ta Bauchi inda suka bayyana kudirinsu na janye dan majalisa Dogara saboda rashin nuna damuwa da zaman lafiyar yankin da rashin tabuka wani abu don hada kan jama’ar yankin.
Jagoransu Alhaji Mohammed Aminu Tukur ne ya gabatar da takardar kukan wacce ke bayyana irin korar kare da cin zarafin da kabilar Sayawa suka yi wa Musulmi da sauran kabilun da ke zaune a garin Tafawa balewa wadanda suka kai kashi 85 cikin 100.
Ya ce, ’yan kabilar Sayawa sun kone garin tare da kashe daruruwan mutane da lalata gidajensu, kuma duk da kokarin gwamnati na samar da zaman lafiya lamarin ya gagara, har sai da ta kai ga Sayawa sun kore kowace kabila ta Musulmi a garin Tafawa balewa ba tare da wani kokarin daidaitawa daga dan majalisa Yakubu Dogara ba.
Alhaji Aminu Tukur ya ce a 1995 da 2001 da 2011 ’yan kabilar Sayawa sun kashe jama’ar Musulmi masu yawa ciki har wadanda suka fito daga kabilarsu, har ta kai gwamnatin Jihar Bauchi ta gaji da rikicinsu ta dauke hedkwatar karamar hukumar zuwa Bununu inda ake zaune lafiya. Ya ce jama’ar yankin sun gaji da tashin hankali, kuma kowa ya san tunda aka koma Bununu ba wani ma’aikacin da ke zaune cikin taraddadi kowa na gudanar da aikinsa cikin kwanciyar hankali, amma sai ga shi dan majalisa Dogara na neman mayar da mutane cikin tashin hankali.  
Shugaban karamar hukumar Dokta Ilyasu Aliyu Gital da tsohon shugaban karamar hukumar Alhaji Ibrahim Halilu sun ce gwamnati ta jima tana kafa kwamitocin daidaita tsakanin jama’a don a zauna lafiya a Tafawa balewa amma ’yan kabilar Sayawa ba sa zuwa ko kuma idan an fara samo hanyar maslaha sai su fice daga kwamitin su nuna ba sa kaunar wani Musulmi a garin.
Ya ce an sha tambayarsu ko akwai wani da ke bata musu rai idan sun zo aiki a Bununu amma har yau sun kasa nuna ko mutum guda.