Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Amfani da kayan gwamnati a yakin neman zabe

A halin yanzu dai yakin neman zabe ya kankama sakamakon dage takunkumin da hukumar zabe ta yi wanda ya bai wa ’yan takara damar himmantuwa wajen tallata kansu domin samun goyon bayan jama’a a zabe mai zuwa.

Sai dai kuma da yake wannan gwamnatin ta himmatu wajen yaki da cin hanci da rashawa da nufin kamanta adalci da gaskiya a harkokin yau da kullum, akwai bukatar gwamnati ta nuna misali hatta a harkokin da suka shafi yakin neman zabe.

ADVERTISEMENT

Zai yi kyau jami’an gwamnati da suke neman sake tsayawa takara tun daga Shugaban Kasa zuwa kansila su tabbatar ba su yi amfani da kayan gwamnati ba a yayin gudanar da yakin neman zabensu. Yin haka zai nuna cewa ana shirin yin adalci a zabe mai zuwa kamar yadda Shugaban Kasa Buhari ya yi alkawari, domin babu wanda aka fifita a cikin ’yan takara masu mukaman gwamnati da wadanda ba su rike da wani mukami.

Wannan tsarin shi ne shugabannin da suka gabata irin su Firimiyan Arewa Sa Ahmadu Bello, Sardaunan Sakkwato suka yi amafani da shi a yayin gudanar da yakin neman zabensu a Jamhuriyya ta Farko, wanda ya sanya har zuwa yau ake ganin girmansu saboda adalcin da suka shimfida a lokacin da suke mulkin kasar nan.

ADVERTISEMENT

Alhaji Ali Sarkin Mota, babban direban Sardauna, yana nan da rai a Unguwar Sarki da ke Kaduna shi ne ya bayyana mini yadda Sardauna yake gudanar da yakin neman zabensa, inda ya ce marigayi Sardauna Ahmadu Bello ba ya amfani da motocin gwamnati idan zai fita harkar siyasa, maimakon haka tasa yake dauka a fita yakin neman zabe.

Saboda haka ya kamata shugabannin yanzu da ke yaki da rashawa da cin hanci tare da kokarin ganin an tabbatar da adalci ga kowa a zabe mai zuwa su yi koyi da halayen shugabannin farko wajen ganin ba su fifita kansu a kan sauran ’yan takara ba.

Bai kamata shugabanni su rika yin amfani da kayan gwamnati tamkar kayansu na kashin kansu ba. Kamata ya yi su yi koyi da dabi’un shugabannin da suka gabata, misali dattijo marigayi Yahaya Gusau ya shahara wajen rike amana da gaskiya domin shi ma ba ya amfani da kayan gwamnati wajen gudanar da harkokinsa na kashin kansa, inda aka bayar da misali da wata mota da masaka ta ba shi a lokacin da yake shugabancinta amma bai taba amfani da ita a harkokin da ba su shafi masakar ba. Hatta marigayi Dan Masanin Kano Alhaji Yusuf Maitama Sule wanda ya yi aiki tare da Yahaya Gusau tun a Jamhuriyya ta Farko kuma ya san shi sosai, ya taba bayyanawa a 1990 yayin da aka kaddamar da asusun neman taimakon raya gidan tarihi na Arewa (Arewa House) a Kaduna a yayin da aka nada Alhaji Yahaya Gusau a matsayin ma’aji wanda zai ajiye kudin da aka tara, inda Dan Masani ya ce,  ‘Lallai an damka kudin a hannun wanda ba za su salwanta ba.’

Shugabannin da suka gabata ba su dauki kayan gwamnati a matsayin ganima ba, suna ganin kayan gwamnati a matsayin amana ne da ya kamata su kula da su sosai. Shi ya sanya a tarihin Musulunci aka bayar da labarin cewa wata rana Halifa na biyu Sayyidina Umar (RA) sun yi taro a cikin dare aka kunna fitila ta gwamnati, bayan sun kammala taron sai suka ci gaba da hira tasu ta kashin kansu. Sai Sayadina Umar ya kashe fitilar, da aka tambaye shi dalilin yin haka sai ya ce ‘wannan kayan gwamnati ne mun yi amfani da fitilar ce, domin gudanar da aikin da ya shafi gwamnati, tunda mun gama muna wani abin da bai shafi gwamnati ba shi ya sanya na kashe fitilar.’

Wani yanki ne na rashawa a rika amfani da kayan gwamnati a harkokin da ba su shafi gwamnati ba, domin haka wajibi ne jami’an gwamnati su kula, kuma a wannan lokacin ne na yakin neman zabe gwamnati za ta kara nuna cewa lallai da gaske take yi za a gudanar da zabe mai inganci inda za a bai wa kowane dan takara dama daidai da kowa ba tare da fifita wani dan takara domin yana rike da mukamin gwamnati ba. A fagen gwamnati a yi amfani da kayan gwamnati, a fagen siyasa kuma kowa ya yi amfani da kayansa, haka shi ne adalci.

Allah Ya sa a gudanar da yakin neman zabe lafiya ba tare da cin zarafin kowa ko munana wa wadansu ba. Marigayi Alhaji Waziri Ibrahim, shugaban Jam’iyyar GNPP a Jamhuriyya ta Biyu yana yawan fada wa magoya bayansa cewa ‘A yi siyasa ba da gaba ba.’