Da Dumi Dumi

Amsoshin sakonnin masu karatu ta tes da imel

“Assalamu Alaikum Baban Sadik, ina fata ba za ka gaji da ni ba. Na yi karatuna ne a fannin fasahar “D-Ray”, amma kwanakin baya na ji wani likita a gidan rediyon BBC yana cewa, ma’aikata a fannin D-Ray ba su dadewa a duniya saboda mummunar illar sinadaran hasken lantarki, wato: Radiation.  Shin, mece ce gaskiyar wannan al’amari?  – Ali Fancy, Garko, Kano: 08171748500.”

Malam Ali Fancy barka da warhaka. Amsoshin wannan tambaya za su samu ne daga bangarori biyu; na farko kan munanan illolin da ke dauke a cikin nau’in hasken D-Ray, wannan shi ne nau’in hasken da ke cikin fasahar na’urar gano cuta mai suna “D-Ray Machine.”  Bangare na biyu kuma shi ne neman tabbacin ko ma’aikata a wannan fanni suna fuskantar takaitacciyar rayuwa sanadiyyar illonin da ke cikin wannan sinadari na haske.  Amsa tambaya ta biyu kam sai kwararre kan harkar lafiya, kamar yadda ka ji wancan likita ya amsa.

Dangane da abin da ya shafi munanan illolin sinadaran kimiyya da ke cikin wannan nau’i na haske, lallai akwai su da yawa. Kamar yadda in kana tare da wannan shafi, ka ji bayanai cikin kasidar “Haske da Yadda Yake Samuwa,” da kasidar “Makamashi da Dukkan Nau’ukansa,” da kuma kasidar “Hasken Leza da Tallafinsa ga Fannin Likitanci.”  Har wa yau a cikin kasidar “Asali da Tarihin Makamin Nukiliya a Duniya” ma bayanai masu gamsarwa sun bayyana.  Sinadaran da ke dauke cikin wannan nau’in haske dai suna da illa matuka, ba wai ga ma’aikatan kadai ba, hatta ga wadanda ake haskaka jikinsu don gano illolin rashin lafiya da ke addabarsu. Duk da fa’idar da ke tattare da wannan fasaha ta “D-Ray” wasu daga cikin masana suna ganin illolin da ke cikinta sun zarce fa’idar, musamman ma ga jarirai, da mata masu juna biyu, da sauran masu lalura.

Kamar yadda rahoton babban taron koli na Hukumar Lafiya ta Indiya ta tabbatar a shekarar 2008, wannan sinadari da ke cikin hasken D-Ray na dauke ne da manyan illoli ga jikin dan adam ta bangare biyu. Na farko shi ne zahirin jiki, inda hakan ke haifar da cutar sankara ta jini, wato “Blood Cancer” ko “Leukemia.” Wannan na cikin manyan cututtuka da idan har suka kama mutum suka ci shi, a karshe sai an yi masa dashen bargo don samar da sabon jini ga jikinsa. Rashin hakan kan iya salwantar da rayuwarsa, iya gwargwadon yadda cutar ta ci shi. Bangare na biyu kuma shi ne, muddin wannan sinadari ya shiga mace mai juna biyu, hakan na iya shafar jaririn da ke cikinta; ana iya haifarsa a karshe da wasu nau’ukan cututtuka masu illa, ciki har da cutar zuciya.

Wadannan kadan ne daga cikin illolin da ke cikin wannan sinadari da ke dauke cikin hasken nau’in “D-Ray.”  Don haka shawara a nan ita ce: ka je wajen likita don neman karin tabbaci da kuma neman hanyoyin kariya, kamar yadda yake cikin ka’ida a ce tun a makaranta an karantar da ku wadannan hanyoyi.  Da fatan ka gamsu.

ADVERTISEMENT

Salaamun alaikum, Allah Ya kara basira Baban Sadik. Yau kam na gan ka zahiri kana bayani a Sunnah TB, kamar yadda muke karanta bayananka badinan a AMINIYA. –  Adam Umar, Abuja.

Wa alaikumus salam, Malam Adam, ina godiya matuka da addu’arka da na sauran ’yan uwa da na yi ta samu ta shafin Facebook. Hakika Hukumar Talabijin Tauraron dan Adam ta Sunnah TB ta gayyace ni inda aka dauki shiri na musamman da za a ci gaba da daukar nauyinsa har na tsawon shekara guda, mai take: “Hanyoyin Sadarwa na Zamani.”  Bayanai ne kan kwamfuta da Intanet da sauran hanyoyin sadarwa na zamani. Akwai masu sauraro a zauren shirin, wadanda ke yin tambayoyi kan bayanan da muke yi (ni da Malam Salisu Hassan Webmaster, sai mai gabatarwa).  Allah Ya sa mu dace, amin.

Assalamu alaikum Baban Sadik, yaya aiki, yaya jama’a, kuma yaya su Sadik? Ina yi maka fatar alheri. Ka kasance cikin koshin lafiya. Sako daga masoyinka: Yahuza Idris, Hotoron Arewa, Tunshama Kuarters, Ketare, Kano: 08095588320

Wa alaikumus salam, ina matukar godiya sosai Malam Yahuza, Allah Ya saka maka da alheri, amin.  Hakika kana matukar karfafa mini gwiwa da sauran masu aiko sakonni makamantan wannan.  Allah Ya sa mu cika da imani, amin.

Assalamu alaikum, ina son Baban Sadik ya kara mini fashin baki kan yadda ake tsara Mudawwana, wato Blog. Ta yaya zan sa murya da kuma shafin Youtube?  Na gode.  Daga Aliyu M. Sadisu, Minna: aliyusadis@gmail.com

Wa alaikumus salam, Malam Aliyu ai wannan bai da wahala ko kadan. Tunda kana amfani da masarrafar Blogger ne, idan ka shiga shafinka, sai ka matsa Sign In daga can sama a hannun dama, kana gama shigar da bayananka, za a kai ka inda tsare-tsaren shafinka yake ne, kai-tsaye, wato: DashBoard.  Daga nan sai ka je LayOut, inda ake canja wa shafi kamanni da kintsi.  Idan ka samu kanka a can, sai ka matsa alamar Add a Gadget da ke sama daga hannun dama. Shafi zai budo mai dauke da nau’ukan masarrafai masu fa’idantarwa da za ka iya kara wa shafinka. Sai ka zabi wanda kake so. Idan ma ba ka ga abin da kake so ba, duk bai baci ba.  Daga hannun hagu can kasa za ka ga inda aka rubuta: Add Your Own, sai ka matsa, ka shigar da adireshin shafin da kake son karawa, ka matsa Add URL. Ka gama ke nan.  Da fatar ka gamsu.

 

Allah Ya saka da alheri, Ya kara imani. Daga: 08064022965

Amin summa amin, ina godiya matuka da addu’o’inku. Na gode.