✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Amsoshin tambayoyi: Kariya daga sarar maciji

Hanyoyin kariya daga saran maciji A Najeriyarmu ta Arewa an fi samun macizai a jihohin Arewa maso Gabas irin su Bauchi da Gombe da Taraba…

Hanyoyin kariya daga saran maciji

A Najeriyarmu ta Arewa an fi samun macizai a jihohin Arewa maso Gabas irin su Bauchi da Gombe da Taraba da kuma Jihar Filato a Arewa ta Tsakiya, musamman a garuruwan Billiri, da Kaltungo da Alkaleri da Langtang da makwabtansu. Akan samu ma a jihohin Borno da Adamawa. To a bana saboda sanyi ana samun karuwar sarar macizai a wasu yankunanan Arewa inda a yanzu a makarantun kwana, kai har da gidajenmu ake jin bullar matsalar. A da an fi samun wannan matsala ce a tsakanin manoma da makiyaya da mafarauta da masu wasa da maciji, amma a yanzu labarin ya fara yawa a birane wato makarantu da gidaje.

Macizai masu sara da dafi ba su kai marasa dafi yawa ba, domin da yawa za su iya yin sara ba tare da sun saki wani dafi ba. Haka nan ma akwai irin su mesa wadda ba ta sara sai dai ta kama mutum ta nannade a jikinsa ta matse shi ta yadda zai kasa numfashi, har ya ce ga garinku. To amma abin farin cikin shi ne a yankin Kudu aka fi ganin mesa.

Alamomin sarar maciji

Yawanci duk wadanda maciji ke sara maza ne, kuma an fi samun wannan matsala a daji ko a gona. Amma a ’yan kwanakin nan a makarantu da gidajenmu a yanzu akan ji abin yana taba mata. Duk wanda maciji mai dafi ya ciza da fari za a ji dan zafi a wurin, mai tsanani ko marar tsanani dangane da nau’in macijin da ya yi sarar.

A wasu lokuta kuma wurin da aka yi sarar ba ya wani zogi. Za a ga ’yar tsaga a fatar ta inda dafin ya shiga, akan ma iya ganin jini a wurin saboda yawanci dafin macijin kan tsinka jini, ta yadda a wadansu akan ga jini ya yi ta zuba ta kafafe da dama ya ki tsayawa. Akan iya ganin jinin har ta baka a wasu lokuta. Sauran alamun sun hada da firgita da dimaucewa saboda babu tsammani yawanci abin ke faruwa. Da yake duk yawanci dafin macizai laka yake bi, bayan ’yan awoyi mutum kan iya kasa motsi ko magana ko gani ko ji, a wasu lokuta ma numfashi gagara yake yi.

A wasu lokutan macizai kan iya fesa dafi a ido. Idan a ido aka fesa wa mutum dafin nan da nan zai ji radadi ya kuma fara gani dushi-dushi, idan ba a dauki mataki da wuri ba ma har makanta dafin kan sa.

Yana da kyau idan an ga macijin da ya yi sara a kashe shi a tafi da shi asibiti domin a ba da maganin karya dafin wannan nau’in macijin. Idan kuma ba a ga macijin ba za a iya ba mutum maganin dafin jama’un macizai a asibiti. Wato a asibiti akwai maganin dafi iri-iri, akwai na dukkan macizai, akwai kuma na macizai daban-daban. Kusan dukkan wadanda a kan kai asibiti aka ba su allurar da wuri suna rayuwa.

 

Hanyoyin kariya

  1. Manoma da makiyaya da mafarauta su suka fi kowa shiga hadarin samun matsalar, don haka su rika sa takalman roba masu tsayi da kauri (sau ciki) kamar takalmin ruwa ke nan idan za su fita sana’a.
  2. Idan aka ga maciji a gona ko a daji bai kamata a tanka masa ba, canja hanya ake a kyale shi ya wuce. Yawanci tsokana ce ko takura kan sa macizai cizo.
  3. A rika yawo da fitila a hannu da dare musamman ga mutanen karkara masu ratsa ciyayi cikin duhu
  4. A kula da tsabtar muhalli musamman yanke ciyayi da gyara juji a mazauninmu na cikin gari.
  5. Macizai kan ziyarci wuraren da akan samu beraye da kwadi ko da a harabar gidajenmu ko bayan gida, domin wadannan kananan dabbobi sukan iya zama abincinsu.
  6. Akan iya samunsu ma a cikin mazaunin ba-haya na tangaran nannade a hannun mazaunin ta ciki inda za su iya buya da sanyi domin jin dumi, ta yadda ke nan yana da kyau a kwara ruwa a irin wadannan mazaunai kafin amfani da su, musamman a lokutan sanyi.
  7. Ya kamata hukumomi su rika sa alamu na tunatarwa a wuraren da aka san ana samun macizai, a rubuta balo-balo cewa “A yi hankali da macizai!”
  8. Da zarar maciji ya sari mutum a yi sauri a kai shi asibiti domin ba shi allurar da ta dace
  9. Kada a sa kashin dabbobi wato irin takin nan na kashin dabbobi a wurin ciwon kamar yadda wadansu suke yi, don hakan zai iya sa kwayoyin cuta musamman kwayar cutar tatanas mai sa ciwon sarke-hakora ta shiga ciwon. Za dai a iya sa ruwa da sabulu a wanke wurin kafin a isa asibiti.
  10. Za a iya daure saman wurin da abin ya faru don gudun kada dafin ya bi jini. Amma kada daurin ya yi karfi sosai tamau domin yin hakan kan iya sa wa wannan bangare rashin gudanar jini.
  11. Kada kuma a ce za a tsaga wurin da aska ko a ce za a zuko dafin da baki.
  12. Gwamnatocinmu su rika tabbatarwa cewa akwai magungunan dafin macizai a asibitocinmu a koyaushe, domin rashin wadannan magunguna ne ke sa rasa rai, ba harbin ba. Idan aka tabbatar da wadannan magunguna a asibitocinmu za a rage mace-macen da wannan matsala kan haddasa. A kasashen da suka san me suke yi, inda ba su da matsalar macizai ma kamar tamu asibitocinsu kullum suna nan da wadannan allurai, ko da sun lalace akan zubar a kawo wasu, wato ke nan ba a rasa su a kowane lokaci
  13. A yanzu haka hukumomin lafiya na kasa-da-kasa ne kan gaba wajen samar da alluran dafin macizai a asibitocin yankunan da suke da yawan macizai, saboda a yi saurin ba wa marar lafiya.

Na kasance ina yawan jin dumi a wannan lokaci na sanyi. Shin ko hakan matsala ce?

Daga A.B.A Pandogari

Amsa: A’a ba wata matsala, ai haka jiki yake so dama. Lokacin sanyi ya bukaci dumi, lokacin zafi ya bukaci sanyi

Shin ko ciwon sanyin kashi na da alaka da wani ciwo mai sa jijiyon kafa da na cinya firfitowa?

Daga Khalil M.A

Amsa: A’a ba su da alaka, shi ma firfitowar jijiyoyin kafafuwa ciwo ne mai zaman kansa da muke kira baricose beins wanda wasu abubuwa kan jawo. Don haka mai samun irin wannan sai ya je an duba dalilin da ya jawo masa matsalar.

Amsoshin Tambayoyi

Ko shin za a iya ba wa yaro dan wata daya man Zaitun?

Daga Hauwa’u Akuyam

Amsa: A’a a likitance ba za a ba wa yaro dan kasa da wata shida komai ba, ko man Zaitun ne, sai dai idan likita ne ya rubuta masa da sunan magani