✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An bude Cibiyar Karbar Koke-Koken Fyade da Makamantansu a Kafanchan

Gwamnatin Jihar Kaduna ta hannun Ma’aikatar Shari’a ta Jihar ta bude cibiyar da za ta rika karbar koke-koken wadanda aka yi musu fyade ko yunkurin…

Gwamnatin Jihar Kaduna ta hannun Ma’aikatar Shari’a ta Jihar ta bude cibiyar da za ta rika karbar koke-koken wadanda aka yi musu fyade ko yunkurin tilasta su don aikata lalata tare da bayar da shawarwari ga wadanda abin ya shafa.

Cibiyar, wacce ayyukanta sun kunshi gwaje-gwaje da daukar nauyin magani da bayar da shawarwari ga wadanda aka yi wa fyade ko kokarin tilasta wani ko wata ta hanyar yin barazana a makarantu ko ma’aikatu, ita ce irinta ta uku a JiharKaduna kuma ta farko a Kudancin Jihar.                                                                                                                                                  An bude ta ce a wani sashi da ke babban asibitin garin Kafanchan don kula da kananan hukumomin Kudancin Kaduna, kamar yadda Babban Sakataren Ma’aikatar Shari’a ta Jihar, Barista Chris Umar ya bayyana yayin kaddamar da sashin a makon jiya.

Babban Sakataren ya koka kan yadda matsalolin da suka jibinci laifuffukan fyade suka yawaita a cikin al’umma inda ya ce daga cikin aikin da cibiyar za ta gudanar har da bayar da taimako na shari’a ta hanyar kai karar wanda aka kama tare da tsaya wa wanda aka yi wa fyaden.

Ya ce bincike ya nuna cikin mata uku, daya ta taba fuskantar wannan matsalar haka namiji daya cikin biyar ya taba shiga cikin matsalar, sai dai ya ce abin takaici shi ne yadda mutane ke jin tsoron bayyanawa saboda gudun tozarci a cikin al’umma inda ya ce shiru a kan hakan shi ke kawo yawaitar lamarin.

A nasa jawabin, shugaban kungiyar da ke gudanar da irin wannan sashi na jihar Kaduna gaba daya, Alkali Darius Khobo ya jinjina wa Gwamnatin Jihar Kaduna kan goyon baya da tallafin da take bayarwa wajen samar da irin wadannan cibiyoyi don dakile matsalolin fyade da kuma bayar da shawarwari game da daukar mataki na shari’a ga wanda aka kama da laifi.

Ya ce ranar da suka bude irin wannan sashi a Zariya sai da suka samu koke-koke bakwai inda ya ce babban abin takaici wadanda abin yafi shafa su ne ’yan kasa da shekara daya zuwa shekara 14.

“Wani lokaci za ka ga malami ya ce sai mace ta bayar da kanta kafin ya ba ta maki a jarrabawa ko kuma sai mace ta ba da kanta kafin a dauke ta aiki a kamfani ko ma’aikata, wanda dukan wadannan suna daga cikin laifuffuka dangin lalata kuma za su iya faruwa ga namiji ko mace,” injishi. Sai ya yi kira ga jama’a su bayar da hadin kai ga cibiyar.

Ya ce kasancewar garin Kafanchan da aka bude sashi don kula da shiyyar kudancin jihar gaba daya ya yi nisa da garuruwan Gwantu da Kauru da ke kananan hukumomin Sanga da Kauru ya sa suke tunanin bude wasu a garuruwan.

Shugabar Riko na Karamar Hukumar Jaba, wacce ta yi magana a madadin shugabannin kananan hukumomi takwas na Kudancin Kaduna, Hajiya Hadiza Usman Mu’azu ta jinjina wa Gwamnatin Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i kan wannan namijin kokari tare da yin kira jama’a da kada su ji kunyar kawo kokensu domin bai wa cibiyar damar gudanar da aikace-aikacenta.

Shugabar Cibiyar ta Kudancin Kaduna, Misis Grace Yohanna ta mika godiyarta ga Allah da samun wannan cibiya sannan ta yi kira ga jama’a musamman wadanda wannan abin ya shafa su rika zuwa don karbar shawarwari da taimakon da zai amfane su maimakon nokewa.

Bikin wanda Sarkin Bajju (Agwom Bajju) Malam Nuhu Bature ya jagoranta, ya samu halartar shugabannin ’yan sanda da na NSCDC da shugabannin kungiyoyin addini da Sarkin Ikulu da wakikan sarakunan Jaba da Kagoro da sauran kungiyoyin al’umma.