✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An ceto mutum 8 daga gidan da ya rushe a Ibadan

Mahukunta a Jihar Oyo sun tabbatar da cewa an yi nasarar ceto mutum 8 daga cikin buraguzan wani gida mai bene uku da ba a…

Mahukunta a Jihar Oyo sun tabbatar da cewa an yi nasarar ceto mutum 8 daga cikin buraguzan wani gida mai bene uku da ba a kammala ginawa ba wanda ya rushe a ranar Juma’a da ta gabata a Unguwar Bode a birnin  Ibadan.

Dukan mutanen da aka ceto suna leburanci ne a rusasshen gini. Tuni aka garzaya da mutanen zuwa asibitin Gwamnati na Adeoyo domin kula da lafiyarsu kyauta kamar yadda Gwamna Abiola Ajimobi na Jihar Oyo ya bayar da umarni. Da yake tausaya wa wadanda hadarin ya rutsa da su cikin wata takardar sanarwa da mai ba shi shawara na musamman a kan harkokin sadarwa Mista Bolaji Tunji ya sanya wa hannu, Gwamna Ajimobi ya ce, gwamnatinsa za ta nada kwamitin bincike domin gano musabbabin rushewar ginin. Ya ce duk wanda aka samu da hannu wajen yin sakaci ko makamancin haka za a hukunta shi kamar yadda doka ta tanada.

Gwamna Ajimobi ya jinjina wa ayarin masu aikin ceto da suka hanzarta kai agajin gaggawa suka ceto mutanen. Ya yi godiya ga Allah da Ya sa babu wanda ya rasa ransa a ruftawar.

Daya daga cikin mutanen da aka ceto, mai suna Toheeb Gbadamosi mai shekara 19 cewa ya yi, “Yau ne ranar farko da na fara aikin leburanci a wannan wuri domin samun dan abin da zan ciyar da kaina da sauran bukatun yau da gobe. Ina godiya ga Allah da Ya tserar da ni.”

Wani da al’amarin ya auku a kan idonsu da ya nemi a sakaya sunansa cewa ya yi, “A daidai lokacin da wannan gini ya fara rushewa akwai mutane masu yawa da muke gudanar da wasu abubuwa a kusa da wannan wuri, amma mun kasa kai agaji saboda tsoron kada abIn ya hada da mu. Amma wadansu daga cikinmu sun yi amfani da wayoyi suka rika kiran ofisoshin jami’an Hukumar Kashe Gobara da ’yan sanda wadanda suka amsa kiran tare da kawo agajin gaggawa lamarin da ya sa aka fara ceto wadanda suka makale a cikin baraguzan ginin.”

Wani ma’aikacin kashe gobara da ya ki fadin sunansa, ya shaida wa ’yan jarida cewa, babbar matsalar da suka fuskanta a lokacin da suke gudanar da aikin ceto rayukan mutanen ita ce, rashin kayan aiki na zamani da ake amfani da su wajen daga buraguzan gini da duwatsu daga wannan sashe zuwa wancan.

Ya ce, “Hakan ne ya sa aikin namu ya yi jinkiri zuwa cikin dare amma mun yi iyakar kokarinmu tare da taimakon jama’a mun ceto dukan mutanen babu wanda ya rasa ransa a cikinsu.”