Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

An dage shari’ar Alkalin Alkalan Najeriya Walter Onnoghen

Kotun da’ar ma’aikata (CCT) ta dage zamanta na sauraron shari’ar da ake wa Alkalin Alkalan Najeriya Mai shari’a Walter Onnoghen, bayan ya ki bayyana a gaban kotun yau Litinin zuwa ranar Talata 22 ga watan Janairun 2019.

Bayan mintuna 40 na jiran halartar Alkalin Alkalan Najeriya Mai shari’a Walter, Shugaban Kotun Danladi Umar ya bada umarnin kotun da ta dage zamanta har zuwa ranar 22 ga watan Janairun don ci gaba da sauraran karar.

ADVERTISEMENT

A cewar kotun laifuka shida ne ake tuhumar babban alkalin, dukkanninsu sun shafi kin bayyana dukiyar da ya mallaka.

ADVERTISEMENT