✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An dakile harin makami mai linzami da aka kai ga Kasar Saudiyya

Rundunar sojin saman kasar Saudiyya ta ce ta dakile wasu hare-haren makamai masu linzami biyu da ‘yan tawayen Houthi suka yi yunkurin kai wa biranen…

Rundunar sojin saman kasar Saudiyya ta ce ta dakile wasu hare-haren makamai masu linzami biyu da ‘yan tawayen Houthi suka yi yunkurin kai wa biranen Makkah da Jeddah a ranar Litinin da ta gabata. kamar yadda kafar yada labarai ta Al Arabiya ta ruwaito.

Jaridar Al Arabiya ta ce rundunar sojin saman ta tarwatsa makaman masu linzamin.

Gwamnatin Yemen wadda Saudiyya, ke mara wa baya ta yi Allah-wadai da harin, inda ta bayyana cewa kai hari, birnin mai tsarki “mummunan aikin ta’addanci ne.”

A makon jiya ne  dai ‘yan tawayen Houthi suka fara shirye-shiryen janyewa daga tashar jirgin ruwa ta Hudaydah da kuma wasu kananan tashoshi a yankin, a matsayin mataki na farko tun bayan da aka cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a watan Disamba, daya gabata.

Dukka bangarorin biyu watau bangaren  gwamnati da kuma na ‘yan tawayen na Houthi sun cimma yarjejeniyar barin tashar jirgin ruwan, domin bayar da dama a shigo da kayayyakin tallafi ga alumma.

A kalla fararen hula 6,800 aka kashe a yakin basasar kasar Yemen wanda aka shafe shekaru hudu ana gwabzawa.

Hakazalika yakin ya yi sanadiyar jikka ta mutum 10,700 kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, yayin da dubban mutane suka mutu sakamakon rashin samun ingantaccen abinci, mai gina jiki da kuma kamuwa da cututtuka iri-iri.