Da Dumi Dumi

An doke Usain Bolt a tseren mita 100

A karshen makon jiya ne dan tseren Amurka Justin Gatlin ya doke Usain Bolt dan tseren Jamaika a gasar tseren mita 100.
Gasar wacce da ta gudana a garin Rome da ke Italiya ana yi mata lakabi ne da gasar tsere ta Rome Golden Gala da ta samu halarcin manyan ’yan tseren da ake ji da su a fadin duniya.
An ce Justin Gatlin ya doke Bolt ne da sakan daya (1 second). Yayin da Gatlin ya gama a minti 9 da sakan 94 (9.94 seconds) shi kuma Bolt ya kammala ne a minti 9 da sakan 95 (9.95 seconds).
Usain Bolt ya ce “na yi murna da yadda na fara tseren bayan da aka alkalin wasa ya saki kunamar bindiga sai dai gab da zan kai makura sai na ji wata jijiya ta dan sarke min a karkashin cinyata da hakan ya sa na daga kafa, kuma ina tsammani hakan ne ta sa aka doke ni zan yi duk mai yiwuwa na ga hakan ba ta sake faruwa da ni ba”.
Usain Bolt dai ya kafa tarihin dan tseren da ya lashe zinare shida a gasar tseren Olamfik daban-daban kuma har yanzu ba a samu kamarsa ba a gasar tseren mita 100 da 200.