✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…An hana ni ganin mijina – Matar Ahmed Sakwaya

Ko kina zargin da hadin bakin wasu aka kama mijinki? Ni ina zargin abokan kasuwancinsa ne a nan U&M Motors akwai wani da suke kasuwanci…

Ko kina zargin da hadin bakin wasu aka kama mijinki?

Ni ina zargin abokan kasuwancinsa ne a nan U&M Motors akwai wani da suke kasuwanci mai suna Mallah da shi asali dai shi aka fara kamawa, bayan wata shida da kama shi, sai aka zo aka tafi da mijina Ahmed Sakwaya da abokin kasuwancinsa Garba Alhassan, aka tafi da su wai sun hada kudi sun sayi mota tare da shi wato shi da yake hannun ke nan. Don haka su suka ce mota ce shi ya ce kudi ne, to dole za su tafi da shi, kuma ba na zargin hakan saboda a gaban hukumar kasuwa aka yi komai, don ko lokacin da aka zo kama su shi Garba suka samu ba su samu mijina ba, sai suka yi masa waya DSS sun zo nemansa amma ba su same shi ba sun ta fi da Garba sun ce saura shi. To tunda suka tafi da su gaba daya da zimmar za su yi bincike, har yanzu shiru. Mun ta kokarin mu gan shi har yanzu ba su ba mu dama ba. Yanzu na koma gidan iyayena da zama.