✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An jefi hoton Shugaban kasar Taiwan don a kawar da shi daga mulki

Dubban mutanen kasar Taiwan ne suka yi zanga-zangar neman kawar da shugaban kasarsu daga mulki, inda suka yi ta jifar hoton Ma Ying-jeou da takalma.…

Dubban mutanen kasar Taiwan ne suka yi zanga-zangar neman kawar da shugaban kasarsu daga mulki, inda suka yi ta jifar hoton Ma Ying-jeou da takalma. Masu zanga-zangar sun taru a kofar gidan tarihi na Dokta Sun Yat-sen da ke Taipei babban birnin kasar.
Masu zanga-zangar, wadanda suka fito daga kungiyoyi da dama, sun bukaci Shugabansu, wato Ma, wanda shi ne Shugaban Jam’iyya mai mulki, wato Kuomintag (KMT), da ya sauka daga mulki saboda sakacin da ya yi wajen rushewar tattalin arzikin kasar, tare da fitto da tsare-tsaren gwamanti da suka haifar masa da bakin jini.
An nuna hotunan masu zanga-zangar a tashar talabijin, inda suke rera wakokin da ke nuni da kifar da Gwamnatin Ma Ying-jeoul. Su kuwa wasu daga suka fito daga wani gungun masu zanga-zangar, sun bukaci a rufe kamfanoni da masana’antun kasar.
An fara yi wa shugaban matsin lamba, a lokacin da ma’aikatan kasar da ma suka rasa aikinsu, bayan da ya dauke majalisar kasar daga kasar zuwa kasar Sin, inda ya fake da samun saukin kudin kwadago da filin kasa. Fiye da mutum dubu suka taru a wani dandali da ke gaban ofishin shugaban kasa, a Taipei. Ma ya samu nasarar lashe zabe a shekarar 2008, bayan da ya samu nasarar kyautata danganata harkokin kasuwancin kasar da yawon bude idanu da kawar adawarsu, wato Sin. Sai kuma aka sake zabarsa a karo na biyu, inda zai sake shafe shekaru hudu a kan karaga sakamakon nasarar da ya samu a shekarar 2012.