✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai unguwa a kan badakalar fili

Hukumar ’Yan Sanda a Jihar Ogun ta ce ta kama wani mai unguwa da ke yankin Ifo a jihar, wanda ake zargi da badakalar fili…

Hukumar ’Yan Sanda a Jihar Ogun ta ce ta kama wani mai unguwa da ke yankin Ifo a jihar, wanda ake zargi da badakalar fili na Naira Miliyan 15 da rabi.

Mai magana da yawun hukumar ’yan sandan jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi ya shaidawa Aminiya cewa kame mai unguwar ya biyo bayan takardar koke da kamfanin Jadmat ya shigar a ofishin ’yan sanda wanda ya bayyana cewa kamfanin ya sayi fili Hekta 23 akan Naira miliyan 15 da rabi a wajen mai unguwar, bayan da kamfanin ya biya kudin sai mai unguwar ya yi ta sayar da sashen filin, inda kafin kamfanin ya farga mai unguwar ya sayar da Hekta 17 cikin 23 da ya sayarwa kamfanin tun da fari.

Abimbola Oyeyemi ya ce biyo bayan binciken Da Kwamishinan ’Yan  Sandan Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu yasa aka gudanar, lamarin da ya sanya aka kame mai unguwar wanda ya amsa laifinsa, ya ce ya sayar da sashen filayen da ya riga ya sayarwa kamfanin tun da fari ne saboda kudin da yake bukata domin gudanar da bukukuwan wankan sarautar da aka ba shi, ya ce rundunar zata gurfanar da wanda ake zargi a kotu da zarar ta kammala bincike.