✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama tsoho mai shekara 64 kan yin damfara a Jigawa

Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekara 64 mai suna Sa’id Adamu mazaunin kauyen Rijana a Jihar Kaduna da dansa Zubairu Adamu Rijana mai…

Yan sanda sun kama wani tsoho mai shekara 64 mai suna Sa’id Adamu mazaunin kauyen Rijana a Jihar Kaduna da dansa Zubairu Adamu Rijana mai shekara 26 bisa zarginsu da damfarar wani yaro abokin dansa mai suna Rabi’u Nuhu mai shekara 28 wanda dansa ya kira daga Agege a Jihar Legas.

Matashin ne ya dauki mahaifinsa da wancan abokin nasa zuwa Birnin Kudu domin su yi harkar canjin Dalar Amurka a wajen wadansu mutum hudu wadanda yanzu haka suka tsere.

Wanda aka kira daga Legas din ne ya kai korafi wajen ’yan sanda cewa sun amshi kudinsa  Naira miliyan daya, aka canja masa da Dalar Amurka ’yan dari-dari guda 175 wanda ya yi daidai da Naira miliyan shida, inda ya ce bayan musayar kudin ne mutanen suka bace bai gansu ba.

Kwamashinan ’Yan sanda Bala Sanchi ya tabbatar da haka, inda ya ce lamarin ya sa ’yan sanda suka kama Zubairu Sa’id da mahaifinsa Sa’id Adamu da dan acabar da ya kai su wajen da suka samu masu jabun Dalar wato Auwalu A. Bello mai shekara 30. Kuma ya ce ’yan sanda suna ci gaba da bincike da zarar sun kammala za su gurfanar da su a gaban kotu.

Da yake bayani, Sa’id Adamu Rijana ya ce bai san ’yan damfara ba ne, domin dansa ne ya ce masa wancan yaron yana sana’ar canji shi ne ya kira shi domin shi ma har ya sa gidansa a kasuwa yana son ya sayar ya canji Dalar ta miliyan daya. Ya ce Allah ne Ya taimake shi ba shi za a damfara ba.

Daga karshe Kwamishinan ya hori masu neman canji su guji shiga wurin da ba jama’a, “Duk wanda ya ce ku je daji domin harkar canji, ku yi gaggawar sanar da ’yan sanda,” inji shi.