✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An karrama Sadaukin Zazzau a Jami’ar ABU da ke Zariya

A ranar Asabar da ta gabata ce wakilan Daliban Jami’ar ABU, (Students Representatibe Council -ABUSRC) suka karrama Sadaukin Zazzau Alhaji Yusuf Shehu Idris. An karrama Sadaukin…

A ranar Asabar da ta gabata ce wakilan Daliban Jami’ar ABU, (Students Representatibe Council -ABUSRC) suka karrama Sadaukin Zazzau Alhaji Yusuf Shehu Idris.

An karrama Sadaukin Zazzau din ne a wani taron kara wa juna sani da daliban suka shirya domin wayar da kan matasa kan siyasa da ci gaban kasa mai taken; “Rawar Matasa a Harkokin Siyasa da Ginin Kasa.”

Wannan ne karo na shida da wakilan daliban suke shirya wannan taron kara wa juna sani da suke yin shekara-shekara.

Taron ya samu halartar manyan malaman Jami’ar ABU da wadansu daga wajen jami’ar da masu rike da sarautun gargajiya da ’yan siyasa da kungiyoyin matasa, sannan Sadaukin Zazzau, Alhaji Yusuf Shehu Idris ya zama Uban Taro.

Kungiyar ta ce dalilban sun karrama Sadaukin Zazzau ne bisa lura da yadda yake ba daliban jami’ar gudunmawa da kuma yadda yake taimakon matasa a Zariya da Jihar Kaduna baki daya.

Wakilan daliban sun bayyana Sadaukin Zazzau a matsayin mai sauraronsu a duk lokacin da suka je, kasancewa shi ma tsohon dalibin jami’ar ce.

A karshen taron an kaddamar da Mujallar ABU DIGEST, wadda ake yi lakabi da Sardauna Magazine, wadda Sadaukin Zazzau ya jagoranci kaddamar da ita.