Search
Subscribe
An rantsar da Kais Saied sabon Shugaban Tunisiya

Sabon Shugaban Tunisiya, Kais Saied

An rantsar da Kais Saied sabon Shugaban Tunisiya

Sabon Shugaban Kasar Tunisiya Kais Saied ya sha rantsuwar kama aiki shekaranjiya Laraba, bayan gagarumar nasararsa mai cike da mamaki a zaben kasar da ya fafata  da fitattun ’yan siyasar kasar da suka jima suna gwagwarmaya.

Kais Saied, malamin makaranta ne wanda ba ya da wata gogewa a fannin siyasa, nasararsa a zaben Tunisiya ta zo a ba-zata bayan da ya lashe kashi 72 da digo 71 a zaben na watan nan wanda ya zo bayan rasuwar Shugaban Kasar Beji Essebsi a watan Yuli.

Sabon Shugaban na Tunisiya wanda farfesa ne a fannin shari’a yayin bikin rantsar da shi ya sake nanata kudirinsa na mayar da hankali kacokan kan al’amuran da suka shafi ilimi da tsaro da tabbatar da adalci baya ga gyara alakar Tunisiya da sauran kasashen duniya da kuma yakar cin hanci da rashawa.

Babban aikin da ke gaban Kais Saeid wanda ke samun goyon bayan kusan ilahirin matasan kasar, bai wuce magance matsalar tsaron da kasar ke fuskanta ba, matsalar da Kais ya bayyana da rashin ilimin da ke addabar al’ummar kasar.

Da yake karbar rantsuwar kama aikin, Shugaba Saeid ya nanata kalamansa na barranta kasar daga zamowa ’yar koren kasashen duniya, yayin da  ya bayyana duk wani yunkurin kulla alaka da Isra’ila a matsayin cin amanar kasa, kalaman da ake ganin su suka kara masa farin jini da ya kai ga nasararsa a zaben kasar ta Tunisiya.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin