✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rantsar da kantomomin kananan hukumomin Jihar Bauchi

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya rantsar da sababbin kantomomin kananan hukumomin jihar 20. Rantsar da shugabannin kananan hukumomin ya biyo bayan tantance…

Gwamnan Jihar Bauchi Sanata Bala Muhammad Abdulkadir ya rantsar da sababbin kantomomin kananan hukumomin jihar 20.

Rantsar da shugabannin kananan hukumomin ya biyo bayan tantance su da amincewa da su da Majalisar Dokokin Jihar Bauchi ta yi.

Da yake rantsar da su, Gwamna Bala Mohammed ya shawarce su da su guji cin hanci da rashawa kuma su gudanar da aiki tukuru domin samun ci gaban jihar.

Gwamnan ya kuma shawarce su da su zama masu saukin kai kuma su dauki kansu masu yi wa al’umma aiki kuma su zage damtse wajen ganin sun gudanar da ayyukan da za su ciyar da kananan hukumominsu gaba.

Ya roke su da su girmama shugabanni da dattawa da ma al’ummar yankinsu ta hanyar nuna halaye abin misali da kuma gudanar da mulkin da kowa zai ji ba a bar shi a baya ba don samun ci gaba cikin hanzari.

Kuma ya hore su da su tabbatar da tsare lafiya da dukiyoyin al’umma da tabbatar da walwalar a yankunansu.

Da yake jawabi, Shugaban Riko na Karamar Hukumar Tafawa Balewa Mista Kefas Magaji, ya gode wa Gwamnan saboda damar da ya ba su na yi wa jiharsu aiki, sannan ya  yi alkawarin cewa za su yi aiki tukuru.

Wadanda aka nada sun hada Alhaji Yusuf Garba Karamar Hukumar Alkaleri da Alhaji Danladi Danbaba Karamar Hukumar Bauchi da Mista Iliya Habila Karamar Hukumar Bogoro da Alhaji Sale Dumba Karamar Hukumar Dass sai Alhaji Gara’u Adamu Karamar Hukumar Darazo.

Sauran su ne Alhaji Ahmad Abubakar Karamar Hukumar Dambam da Alhaji Adamu Lele Karamar Hukumar Gamawa da Alhaji Abubakar Ado Karamar Hukumar Giyade da Alhaji Shehu Buba Karamar Hukumar Toro da sauransu.