✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An raunata ’yan jarida a zanga-zangar #EndSARS

Akalla ’yan jarida hudu ne aka jikkata a bakin aikinsu a wurin zanga-zangar #EndSARS a Jihar Gombe. Wasu mahara ne ake zargi da kuma raunata…

Akalla ’yan jarida hudu ne aka jikkata a bakin aikinsu a wurin zanga-zangar #EndSARS a Jihar Gombe.

Wasu mahara ne ake zargi da kuma raunata wasu da dama a farmakin da suka kai wa matasan da ke zanga-zanga a yankin Tumfure domin neman a dakatar cin zalin da ’yan sanda ke yi.

Masu zanga-zangar na kuma kira da a magance matsalar tsaro sannan a inganta da kula da bukatun ’yan sanda da sauran ’yan kasa.

Ana cikin haka ne wasu matasa dauke da makamai suka yi musu kawanya suka auka musu da duka, inda suka jikkata wasu, wasu kuma suka sha da kyar.

Daga cikin mutanen da aka jikkata akwai ma’aikacin gidan talabijin na NTA Gombe, Jimmy Dantsafta. wanda aka caccaka masa wuka a sassan jikinsa aka kuma fasa kyamararsa.

Daga bisani an garzaya da shi Asibitin Kwararru na Jihar Gombe don samun kulawa.

Sauran ’yan jaridar da abun ya rutsa da su su ne Shola Shittu, na jaridar The Nation, da Musa Muhammad na gidan talabijin na Channels TV da Chika Udenko na AIT.

Shola da Musa sun yi raunuka, shi kuma Udenko ya kukkuje a jikinsa amma dukkansu ana kula da su tare da sauran wadanda suka jikkata.

Bayan samun hatsaniyar da kusan sa’a guda mutane sun ci gaba da gudanar da harkokinsu kamar yadda aka saba a yankin da sauran sassan garin Gombe.

Duk da haka an jibge ’yan sanda a sassan birnin inda inda suke gudanar da sintiri a motocinsu.