✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake kama wata mata da ta sato yara daga Arewa a Legas

Rundunar ‘yan sandan Legas ta tabbatar da kama wata mata da ake zargi da sato yara maza biyu daga Arewa a lokacin da ta ke…

Rundunar ‘yan sandan Legas ta tabbatar da kama wata mata da ake zargi da sato yara maza biyu daga Arewa a lokacin da ta ke kokarin tafiya da su garin Onitsha.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ya shaidawa Aminiya cewa matar da mijin ta na tsare a hannun hukumar ‘yan sandan, “Yanzu haka yaran biyu na tare da mu.” In ji shi.

Wani wanda ya shaida kame matar mai suna Abba Abdullahi, da ke zaune a kasuwar Alaba Rago ya shaidawa Aminiya cewa, wani dattijo ne ya zo wucewa sai ya kula da matar tare da yaran biyu a tashar Chemis da ke daura da kasuwar duniya ta Alaba, “Dattijon yaji yaran na magana da Hausa ya kuma kula da cewa matar kabilar Ibo ce, duba da abubuwan da suka faru na satar ‘ya’yan Arewa da wasu bata gari aka ce sun yi a Kano, inda suke kai su Kudu maso Gabas hakan ne ya sanya dattijon kin yarda da matar, sai ya kai kara gidan Sarkin Hausawa wanda ya tura mutanen da jami’an tsaro aka kame matar.”

Ya ce, yanzu jama’a na sanya ido sossai a kan irin wannan lamarin tun bayan da aka kame  mutane nan  masu satar yara a Kano.

Matar da aka kama