Da Dumi Dumi

An samu Fam biliyan 1.25 a asusun bankin mabaraciya

Kirki da jinkai na mutanen kasar Lebanon ya mayar da wata mabaraciya hamshakiyar mai kudi, kamar yadda rahotannin da suka fito daga kasar suka nuna.

Hoton Wafaa Mohammed Awad da kuma katin cakin kudi  na asusun ajiyarta a banki ya mamaye shafukan sadarwa na sada zumunta bayan da aka bayyana cewa matar da take bara a birnin Saida na kasar Lebanon ta tara kudin da suka kai Dalar Amurka dubu 900, (da aka kiyasta sun kai Dirhami miliyan 3.3- kimanin Naira miliyan 324)

Idan aka canja wannan kudi zuwa kudin kasar Lebanon, zai zamo mabaraciya tana da fiye da Fam biliyan 1 da miliyan 250 na kudin Lebanon a asusunta na ajiya da ke bankin Jamal Trust Bank. Wannan batu ya fito fili ne yayin da matar take kokarin kwashe kudinta daga bankin zuwa wani bankin sakamakon matsalar kudi da bankin nata yake fuskanta.

Hoton katinta na fitar da kudi a banki da ta sanya wa hannu ranar 10 ga Satumba ya mamaye kafafen sadarwar zamani. Wannan na nuna cewa Awad ta fi mafi yawan masu ba ta sadaka kudi.

 

ADVERTISEMENT

 

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya