Da Dumi Dumi

An tsinci gawar mutum biyu bayan ruwan sama a Akwa Ibom

An samu rahoton mutuwar mutum biyu bayan wani ruwan sama mai karfi da aka yi da ya kai awa daya, wanda ya yi sanadiyyar ambaliyar a manyan hanyoyin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom.

An gano gawar namiji da mace a cikin kwata a layi mai suna Atiku Abubakar lane kusa da gidan man fetur  na GWT a Uyo. An fara ruwan da misalin karfe 5:30 na yamma zuwa 6:45 na yamma a jiya Lahadi.

Wata ganau mai suna Misis Uduak Mbakara  ta ce, an gano gawar wadanda suka rasun ne a safiyar yau Litinin. Daga nan makwabtan wurin suka sanarwa ‘yan sanda gawar mutanen da suka gani.

 

ADVERTISEMENT
Share