✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zabi Fayemi shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya

A daren jiya Laraba aka zabi sabon shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya NGF, kungiyar ta zabi Gwamnan jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, gwamnan ya zama shugaban…

A daren jiya Laraba aka zabi sabon shugaban kungiyar Gwamnonin Najeriya NGF, kungiyar ta zabi Gwamnan jihar Ekiti, Dakta Kayode Fayemi, gwamnan ya zama shugaban kungiyar ne bayan samun amincewar sauran ‘yan takarar da ke neman shugabancin kungiyar lokacin taron da kungiyar ta yi a Abuja.

Gwamna Kayode, zai maye gurbin Gwamnan Zamfara Abdulaziz Yari Abubakar, wanda ya jagoranci kungiyar daga shekarar 2015.

Kungiyar ta zabi Gwamnan Sakkwato Aminu Tambuwal, a matsayin sabon mataimakin shugaban kungiyar, wa’adin su zai fara daga shekarar 2019 zuwa 2021.