✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An zargi jami’an DSS da tafiya da limami a Bauchi

An zargi jami’an DSS da cewa su ne suka tafi da shahararren malamin nan, Imam Idris Abdul’azeez Dutsen Tanshi da ke Bauchi tun ranar Juma’a…

An zargi jami’an DSS da cewa su ne suka tafi da shahararren malamin nan, Imam Idris Abdul’azeez Dutsen Tanshi da ke Bauchi tun ranar Juma’a da ta gabata.

Lamarin da ya haifar da damuwa da zullumi cikin almajirai da iyalan malamin dama al’ummar Jihar Bauchi ba ki daya.

Shugaban Daliban malamin, Mallam Yau Idris ya tabbatar da cewa DSS ne suka tafi da Malamin cikin takardar da ya raba wa manema labarai a Bauchi, inda ya ce, “Imam Dokta Idris Abdulazeez Bauchi ya amsa gayyata ce kawai da Hukumar DS ta yi masa,” inda ya kara da cewa suna kira da cewa kada wata kungiya ta addinin ta fito don yin zanga-zanga ko tashin hankali kan abin da ya faru.

Malam Yau ya kuma yi kira ga jama’a su zauna lafiya da ci gaba dayin addu’a kamar yadda aka saba saboda ana kokarin neman mafita ta hanyar da ta dace.

Ya bayyana yadda lamarin ya faru da cewa, “a ranar Juma’ar da ta gabata bayan da aka sauko daga Jumma’a sai malam ya gabatar da tafsirin Kur’ani mai girma kamar yadda aka saba, bayan ya kammala tafsirin sai wani Jami’in kaya DSS ya zo ya gayyace shi kan cewa za su je su dawo ne kawai, shi ne tun da suka tafi da shi ba mu sake jin wani bayani ba.

“Washegari sai Malam da kansa ya yi mana waya ya ce a kai masa kayayyakinsa guda biyu don za a tafi da shi a Abuja kuma tunda aka tafi da shi ba a ba mu dama sun ganshi ba.”

Dalibin ya yi zargin cewa suna alakanta abin da siyasa saboda kokarin da mallam din ya yi ta yi na wayar da ka al’umma dangane da yadda al’amura suke tabarbarewa a kasar nan.

Duk kokarin da wakilin Aminiya ya yi na jin bakin hukumomin tsaro a Jihar Bauchi bai samu nasara ba.