✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana ci gaba da shari’ar wanda ya kashe ‘yar shekara uku

Babban Kotun Jihar Kaduna ta Biyu da ke GRA Zariya ta tsayar da ranar 15 ga  Janairun badi domin ci gaba da shari’ar da ake…

Babban Kotun Jihar Kaduna ta Biyu da ke GRA Zariya ta tsayar da ranar 15 ga  Janairun badi domin ci gaba da shari’ar da ake yi wa Shehu Usman Bashir kan tuhumar aikata fyade da kisa ga wata yarinya ’yar kasa da shekara uku da haihuwa.

Shari’ar, wanda Mai shari’a Kabiru Dabo ke yi an daga ta ce bayan da shaida na biyar kuma dan sanda mai bincike, Sufeta Emmanuuel Amed ya kammala bayar da shaida kan wanda ake tuhuma, wanda kuma shi ne shaida na karshe a kan wannan shari’a.

Shehu wanda ke zaune a ’Yan Bita Unguwar Liman, Hayin Ojo a Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna, makwabta ne suka ba da shaida kan lamarin, inda suka ce ya yi wa yarinyar fyade tare da kashe ta.

Tun a wancan lokaci ne lauyar gwamnati, Hajiya Jummai Dan’azumi ta shigar da kara a gaban kotun tana tuhumarsa da laifi biyu na fyade da kisan kai a karkashin sashe na 221na Final Kod.

Idan ba a manace ba, kimanin shekara uku da suka gabata jaridar Aminiya ta kawo muku labarin yadda lamarin ya faru a baya kan inda Shehu ya kai yarinyar dakinsa bayan ya yi mata fyade ta rasu, sai ya sa yarinyar cikin kayan wanki ya nade ta ya boye a cikin dakinsa kuma har aka tafi neman yarinyar tare da shi cewa ta bace. To amma a yayin da ake cikin nemanta ce sai mahaifiyar yarinyar ta ce  tana ji a jikinta cewa ’yarta tana dakin Shehu, don haka a duba dakinsa, domin a lokacin da ’yarta ta rako mahaifinta da zai tafi wajen sana’arsa da safe, ta ji lokacin da  Shehu ke gaida mijinta, kuma tun lokacin da maigidanta ya tafi, ’yarta ba ta dawo gida ba.

Ana zargin cewa Shehu ya yi kaurin suna wajen rashin kamun kai, kuma da aka shiga dakin nasa ana dubawa sai ga gawar yarinyar a nade a cikin tsummokara, farjinta duk ya baci da jini, inda daga nan ne aka dauke ta zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika a Zariya inda aka tabbatar da rasuwarta.