✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yan sanda sun tabbatar da sace ’yar tsohon Shugaban Jami’ar ABU

Rudunar ’Yan sanda Jihar Kaduna ta tabbatar da kai hari da ’yan bindiga suka yi gidan tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa…

Rudunar ’Yan sanda Jihar Kaduna ta tabbatar da kai hari da ’yan bindiga suka yi gidan tsohon Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Abdullahi Mustapha tare da sace ’yarsa.

Da yake tabbatar da aukuwar lamarin, Kakakin Rundunar DSP Yakubu Sabo ya ce a ranar Asabar din makon jiya da dare ’yan bindigar suka far wa gidan inda suka yi ta harbe-harbe tare da raunata mai gadin gidan wanda yanzu haka yake asibiti ana yi masa magani.

’Yar da aka tafi da ita mai suna Maryam Abdullahi mai shekara 35, har zuwa lokacin hada wannan labari babu wani bayani da aka samu daga ’yan bindigar.

Yakubu Sabo ya ce maharan sun fuskanci turjiyyar ’yan sanda da ke Samaru inda suka harbe daya daga cikinsu. Daga cikin kayayyakin da aka samu tare da wanda ya rasa ransa akwai bindiga kirar AK 47 da wayar hannu da kuma harsasai masu rai guda 24. Ya ce ’yan sanda sun dukufa domin gano ’yan bindigar don su fuskanci shari’a, saboda haka sai ya bukaci jama’a su samar musu da bayanan da za su taimaka musu.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bindigar su takwas ne kuma an yi kusan awa daya da rabi ana ba-ta-kashi da ’yan bidigar. Majiyar ta ce an samu harsasai kusan 47 a wurin da aka yi artabu da ’yan bindigar.

Da Aminiya ta so jin ta bakin Farfesa Abdullahi Mustapha ya ce ba abin da zai ce sai dai a yi ta addu’a.Farfesa Abdullahi Mustapha yana zaune ne a Unguwar Malam Sule a bayan Kwalejin Koyon Tukin Jirgin Sama (NCAT) da ke Zariya.