✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin dan takarar Majalisar Tarayya da yunkurin yin kwartanci 

A farkon wannan makon ne hukumar ‘yan sanda a Jihar Nasarawa ta ce ta samu nasarar kama dan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa-Eggon da…

A farkon wannan makon ne hukumar ‘yan sanda a Jihar Nasarawa ta ce ta samu nasarar kama dan takarar Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Nasarawa-Eggon da Wamba da Akwanga, Abdullahi Mohammed bisa zargin yunkurin kwartanci.

‘Yan sandan sun ce sun kama shi ne lokacin yake shirin yin lalata da wata matar aure mai suna Halima Abubakar Bashir a wani otel a Abuja.

Wanda ake zargin tsohon mai taimaka wa Gwamnan Jihar Nasarawa ne a kan Harkokin Labin Shanu. ‘Yan sandan sun bayyana cewa ya nemi tursasa wa matar don ya yi lalata da ita ne saboda ya yi mata hanyar samun damar karatu a babbar jami’ar jihar da ke Keffi.

A nata bangaren, da take bayyana wa ‘yan sanda yadda lamarin ya faru, Halima Abubakar Bashir wace ke Tudun Wada a Karamar Hukumar Keffi a jihar, ta ce sun hadu da Abdullahi ne a ofishin wani jami’i a Jami’ar Keffi lokacin da suka je tare da kanen mai gidanta, don nema mta gurbin karatu.

Ta ce “Muna jiran mai ofis din ne sai shi Abdullahi Mohammed ya shigo, inda bayan ya bukaci ya san abin da muke jira a ofishin, sai kanin mai gidana ya bayyana masa bukatarmu bayan ya gabatar dani gare shi a matsayin matar yayansa. A nan take sai ya bukaci in ba shi lambar wayata, inda ya yi alkawarin cewa zai kira ni. Ya kuma tambayi fannin karatun da nake so a jami’ar.

“To bayan wannan haduwar ne yake ta kirana a waya yana mini kalaman soyoyya da maganganun da ba su dace ba. Sai na ja hankalinsa cewa ni fa matar aure ce, ya kama girmansa da mutuncinsa. Dana fahimci haka sai na gaya masa cewa ba na bukatar yin wata alaka da shi, don duk wani abu bayan haka ba zai yi wa dukkanmu dadi ba. Daga nan sai ya ce shi fa yana da damar neman duk abin da yake so, yana kuma cewa nan ba da dadewa ba zan nemi taimakonsa gwiwata a kasa ina rokonsa.

“Ya ce wai a yanzu ma ya yi nasara a zaben fidda gwani, shi ne dan takarar Majalisar Wakilai na APC kuma wai kodashike ya bar aiki da jami’ar ya shiga harkar siyasa, amma har yanzu yana da iko a jami’ar. Kuma wai zai tabbatar mini cewa idan bai amince in yi karatu a jami’ar ba babu wanda ya isa ya dauke ni,” a cewarta.

Ta kuma kara da cewa, “Don haka wai dole ne in rika ba shi goyon baya muddin ina so bukata ta biya. To sai na sanar da mai gidana abin da ke faruwa, sai mai gidana ya ce idan ya ci gaba da kirana in sanar da shi, zai dauki matakin hukuma a kansa.

“To sai ya kira ni wata rana ya ce min in gaya wa mai gidana cewa ya hada ni da direba mu je mu ga wani mutum da a cewarsa zai taimaka min in samu damar karatun, kuma ya ce idan na tashi zuwa in bar wata takarda da gangan saboda bayan mun zo sai in ce wa direban ya koma gida ya je ya kawo min takardar kamar dai yadda muka shirya da shi kafin na bar gida. Na yi kamar yadda ya bukace ni. Washegari na sanar da magidana, sai ya ce in gaya masa cewa ya zo da kansa ya dauke ni, a inda zai hange shi a kusa da gidanmu.

“Da ya kira sai na ce ya zo ya same ni, bayan wani lokaci sai ya zo ya dauke ni da motarsa. A lokacin bai sani ba cewa mai gidana da wasu jami’an suna biye da mu a baya. Da muka isa wajen binciken sojojin sai suka tsaida mu suna tambayarsa abin da yake yi da matar aure a cikin motarsa, inda shi kuma bai yi gardama ba ya amince da laifinsa,” inji Halima.

A nasa bangaren, wanda ake zargin Abdullahi Mohammed ya tabbatar da dukkan abinda matar auren ta fada, har ma ya kara da cewa, “Na gaya mata cewa bana tsoron mijinta, don haka kada ta damu. Kuma na yi niyar kai ta wani otel ne a Abuja don mu tattauna.”

Da aka tambayeshi ko wannan shine karo na farko da haka ya faru tsakaninsa da matan aure sai ya ce shi ne karo na biyu da ya yi yunkurin yin lalata da ita. Sannan sai ya yi kira ga abokan aikinsa dake jami’ar da su dubi abin da ya faru da shi su daina irin wannan rayuwa don kaucewa fuskantar irin wannan wulankanci da yake ciki a yanzu.

Wakilinmu ya tuntubi Shugaba Mai Kula da Harkokin Malaman Jami’ar, Mista Abraham Ekpo don jin ta bakinsa dangane da aukuwar lamarin, ya tabbatar da cewa lalle Abdullahi Mohammed malami ne a jami’ar sai dai a cewarsa ya bar jami’ar tun kwanakin baya ya shiga harkar siyasa. Saboda haka a cewarsa a yanzu duk abin da ya same shi babu ruwan jami’ar, domin yana zamar kansa ne. “Ko a lokacin da yake tare da jami’ar nan ma ba yana sashen bayar da takardar shiga jami’a ba ne, kuma ba shi da wata damar samar wa wani ko wata wannan damar. Kuma har kawo yanzu babu wanda ya kiramu daga wani waje dangane da batun, kuma abu ne daya faru a wajen jami’ar nan ba a cikinta ba” inji shi.

Sai da a nata bangaren, kungiyar yakin neman zaben dan takarar da ake zargi ta musanta zargin da ake yi wa Abdullahi Mohammed, inda ta ce wannan aikin mahassada ne wadanda ke son bata sunan dan takararsu a siyasance.

Daraktar kungiyar, Inocent Pade ne ya bayyana haka a lokacin da wakilinmu ya tuntube shi dangane da batun, inda ya ce “Game da batun, inaso in bayyana wa duniya baki daya cewa wannan zargi da ake yi wa sabon zababben dan takararmu mai neman wakiltar Nasarawa-Eggon da Akwanga da Wamba a majalisar wakilai ta tarayya, Honorabul Abdullhai Mohammed zargi ne mara tushi balle makama. Don haka muna sanar da jama’a cewa sunan dan takararmu ne ya zo daya ne da na wanda ake zargi, amma ba shi ba ne.”

Shi ma a nasa bangaren, Kakakin APC na Nasarawa, Sam Agidi ya ce ba shakka jam’iyya a jihar ta samu wannan batun zargi da jami’an tsaro ke yi wa Abdullahi Mohammed, sai dai ya ce jam’iyyar ba zata iya yin komai ba tunda maganar tana hannun ‘yan sanda, sai sun kammala bincikensu sun tabbatar da laifinsa kafin su san matakin da zasu dauka a kansa.

Game da irin matakin hukunci da jam’iyyar zata dauka akan wanda ake zargin idan aka sameshi da laifin, kakakin jam’iyyar ya ce “Kamar yadda ka sani shi yake rike da tutar jam’iyyarmu a mazabar kuma jam’iyyar tana da dama ko iko ta canja ta kawo wani daban, don ya maye gurbinsa. Don bazamu bari ya lalata wa jam’iyyarmu suna ba. Don zamu iya rasa kujerarsa idan muka bar shi ya tsaya takarar, bayan an kama shi da laifin.