✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ashe Turawa mutane ne? (3)

Ba ma wani abu ne ya farkar da ni ba sai yawan motsi da kuma kalaman ‘yes what do you want’ da kuma ‘thank you’…

Ba ma wani abu ne ya farkar da ni ba sai yawan motsi da kuma kalaman ‘yes what do you want’ da kuma ‘thank you’ da ‘you are wellcome’. Ganin yadda Turawan ke fadar wadannan kalamai suna bi layi-layi, kwararo-kwararo ya ba ni dariya, domin kuwa na tabbata ba su san abin da suke fada, idan kuma sun sani, kila sun haddace ne kurum, domin kuwa da alama abin da suke fada ba shi e a zukatansu ba. Idan kana kallonsu za ka ga cewa suna cewa ‘me kake so’ cikin murmushi, amma ba annunri a fuskokinsu, suna cewa ‘na gode’, amma ba alamun godiya a fuskokinsu, suna cewa da kai “ sannu kadai ko maraba’, amma ba tabarma a hannunsu. Sai daga baya da suka dawo rarraba lemo da ti na dara fahimtar cewa ai wadannan turawan haka suke kamar butunbutumi, duk abin da suke fada, suna fada ne kurum, ban tabbata ko sun amince da shi ba. Sai da na isa Ingila ne na ga ko’ina kalaman ke nan, na kara fahimtar cewa, al’ada ce kurum, ana fada ne ba wai don an amince da tunanin ba, kamar dai mu ne da ‘ina kwana’, ‘ina wuni’ ko da kuwa muna gaisawa da makiyanmu ne ko abokan adawa.

Kusan dai awa biyar muka yi a sama, ko dai mu yi sama sosai ko mu dawo kasa kadan, wata sa’a muna iya hangen kasa ko dai malelan ruwa ko alamun dazuzzuka, sai dai abin jin dadi shi ne kana iya bin yanayin tafiyar jirgin tun daga barin mu Abuja har zuwa London. A gaban kujerata akwai talbijin mai nuna sinima kala-kala, tana kuma nuna mana taswirar inda muke da sauran awoyi da kilomitoci ko mil-mil da ya rage mu isa London. Kana ganin yadda muke wuce sararin samaniyar kasashen da ke kan hanya, ga mu nan mun wuce Habasha, mun shiga Maroko, mun ratsa kogin da ya raba Afirka da Turai, ga mu nan mun taso wa Turai, mun wuce Andalus, mun kama hanyar Ingila, mun shigo Ingila.

Ga mu nan mun kama hanyar birnin London, mun shigo sararin birnin; ni dai ina biye da taswirar nan kamar addini, sai da na ji matukin jirgin na cewa ‘wadanda ke hagu da ni idan sun leka za su hangi kogin Thames na birnin London a kasa,’ sa’annan na dawo ga jirgin, na hanga sosai na ga London daga kasa, abin da ya zo mani a zuciya shi ne su har yanzu a Ingila kiliya hannun hagu ne, domin motocin da ke tafiya a kasa duk ta hagu suke kiliya. Wani abu kuwa da ya sake zo mani a zuciyar shi ne ga ni ga Turawan Mulkin Mallakar Nijeriya, ko yaya za ta kaya? Sai mun sauka, ma ji yadda ta kaya!

Sauka daga sama ba ta zama mana matsala ba, ta yaya za mu yi maganar matsala alhali tun da muka taso daga Abuja ba wata tangarda ko matsala da muka fuskanta. Ni dai har muka iso birnin London ban ji inda jirgin ya yi wani motsi na tayar da hankali ba, na dauka ma cikin gidana nake, domin kuwa ban a komi daga kallon talbijin sai kallon taswirar inji da ke gabana, sai kuwa wake-wake da ke fita daga rediyo da ke boye, ka sa lasifika a kunne ka yi kwasar sauti iri-iri.

Bayan gida kuwa ai ba bayan gidan kurum yake ba, ga shi nan a tsakiyar daki kowa ke so sai ya leka, yawo kuwa a cikin jirgin sai inda ka tsaya ko inda aka ce ba a shiga, amma mike kafafu bai zama matsala ba. Inda matsalar ta somo shi ne wajen saukowa daga jirgin, domin da muka iso filin jirgin Heathrow da ke London da misalin karfe 3 saura minti biyar kamar yadda yake rubuce a cikin tikitinmu, mun dauka cewa ai sai gida kurum, to ba haka abin ya kasance ba. Mun yi  awa shidda da minti 25 a sama, amma sai da muka yi kusan awa biyu a filin jirgin saman kafin mu fito daga cikin jirgin da kuma kammalawa da ‘yan kastom da migireshin.

Ba wai wata matsala ba ce irin ta lalacewar jirgi ko halin ‘yan kasar ko kuma an nuna mana wani bambanci ko son kai ko makamancin haka, ko alama! Abu na farko dai shi ne ko da muka iso filin jirgin na Heathrow cike yake kamar kullum, da ma kafin mu iso na sami bayanin cewa akwai cunkoso a filin jirgin.

Shi dai wannan filin jirgi yana daga cikin filayen jirgin sama na duniya da ya fi kowane arangama da jirage da kuma fasinjoji, kusan duk minti guda sai jirgi ya sauko ko kuma ya tashi. Saboda haka ko da muka iso matukin jirgin cewa ya yi da mu, sai mun dan yi hakuri domin akwai cunkoso, an ce da shi ya jira daga bakin inda ya dira na dan wani lokaci. Mu dai muna nan a cikin jirgi sama da minti 30, can sai ka ji jirgin ya motsa, ya dan yi gaba na wani lokaci, sai ya tsaya kuma na wani dogon lokaci, kamar dai wanda ya hadu da go- sulo a Legas ko bakin  titin Ahmadu Bello da ke Kaduna ko kuma bakin Bata a Kano. Da yake jirgi ne ba mota ba, sai abin ya ba ni dariya, na ga ga mu a birnin London amma ba hanyar fita.

Da na gaji da sauraren rediyo sai na koma kallon waje in ga me ke faruwa, nan ne na fahimci cewa ai ba laifin jirgin ba ne, ba kuma na ‘yan kamisho ko yuniyon ba ne ( ina dariya) kamar wanda ke tashar Kuka a Kano ko Kawo a Kaduna), inda direba ko ‘yan yuniyon ke yin yadda suka ga dama da fasinja. Nan dai ga mu zazzaune, jirage kuwa wannan ya tashi, wani na biye, wani na sauka, wani na biye, har ta kai ina tunanin yaya ake ba sa yin karo da juna ko kuma su fado wa juna, ganin cewa kusan a cikin kowane minti ne abubuwa ke aukuwa

Za mu ci gaba.