✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ba Azumi ne ya janyo tashin farashin kayan gwari ba -shugabannin kayan gwari

Shugabannin bangarorin tumatir da albasa na kasuwar kayan gwari ta Mil 12 da ke Jihar Legas sun  dora alhakin tashin farashin kayan miya kan yanayin…

Wani sashe na ’yan tumatir da ke kasuwar Mil 12Shugabannin bangarorin tumatir da albasa na kasuwar kayan gwari ta Mil 12 da ke Jihar Legas sun  dora alhakin tashin farashin kayan miya kan yanayin kasuwa, ba lokacin azumi ba, kamar yadda wasu ke tunani.
Shugaban bangaren tumatir, Alhaji Yahuza Alasan ya bayyana wa Aminiya cewa ba su da hannu dangane da tashin farashin tumatir a Legas.
Ya ce, “Gaskiya ba zuwan azumi ba ne ya sa tumatir ya tashi, yanayi ne na kasuwa. Kafin azumi ya zo ba mu da filin sauke kaya, wannan shi ya janyo mana cikowar kaya, amma tunda muka gyara filin da muke sauke kaya, sai tumatir din ya tashi saboda alwus din da aka samu a filin da muke sauke kaya. Ka ga tumatir dan Arewa ana sayar da kwando Naira dubu 11 zuwa dubu 12; dan Jos ana sayar da kwando daga Naira dubu 11 har zuwa 13. Wani lokaci ma har dubu takwas ana samunsa. Tsakanin Alhamis da Juma’ar da ta wuce, farashin ya tashi, domin kafin azumi ya kai dubu biyar zuwa dubu bakwai. Ita gwari ta bambanta da sauran kayayyaki, cikin awa daya ko biyu farashi yake tashi kuma ya sauka”.
Shi ma mataimakin shugaban bangaren albasa na kasuwar, Alhaji Wadata Musa ya ce albasa tana da wuyar ajiya, ba kamar sauran kayan gwari ba. “Gaskiya farashin albasa ya tashi. Kuma lokaci ne ya janyo tashin farashin ta ba azumi ba, domin ita albasa tana da wuyar sha’ani. Noma ta ake yi da yawa a ajiye ta, sai lokacin sayar da ita ya zo a fito da ita a sayar. Babu inda za a iya ajiye ta sai Arewa domin ana yi mata hikima ne yadda ruwa ba zai taba ta ba. Saboda haka tsadar ta ta zo daidai da lokacin da ake ajiye ta a Arewa. Kafin azumi, ana sayar da buhu daga Naira dubu 12 zuwa 13, amma yanzu ana sayar da babban buhu Naira dubu 13”. Inji shi.
Wata mata da ke sayen kayan miya, yau da gobe a kasuwar, mai suna Lateefa ta bayyana takaicin yadda farashin kayan gwarin ke yin tashin gwauron zabo a Jihar Legas.