Search
Subscribe
Ba Shugaba Buhari ne yake bayar da arziki ba – Sheikh Jingir

Shugaban Qasa Muhammadu Buhari

Ba Shugaba Buhari ne yake bayar da arziki ba – Sheikh Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, Sheikh Muhammad Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa Allah ne Yake bayar da arziki, ba Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ba, kamar yadda wadansu suka dauka.

Sheikh Sani Yahya Jingir, ya bayyana haka ne a lokacin da yake gabatar da nasiha a Masallacin Juma’a na ’Yan-taya da ke garin Jos a ranar Juma’ar da ta gabata.

Ya ce duk wanda ya ce Shugaban Kasa Buhari ne yake bayar da arziki, imaninsa bai cika ba. Domin babu mai bayar da arziki sai Allah da Ya yi halitta.

Ya ce “Wallahi da yadda Shugaban Kasa Buhari yake so ne, da yanzu babu sauran matsalar tsaro a Najeriya kuma da yanzu ayyukan hanyoyin mota da sauran abubuwan kyautata rayuwar al’umma sun cika kasar nan. Don haka mu yi hankali da miyagun ’yan siyasa masu bata tunanin mutane. Wallahi gara yanzu da lokacin da ake jefa mana bama- bamai a kasar nan. Don haka gwamnatin Shugaban Kasa Buhari, ta fi gwamnatin da ta gabata,” inji shi.

Sheikh Jingir ya nuna goyon bayansa kan rufe kan iyakokin kasar nan, don hana shigo da miyagun kwayoyi da makamai da shinkafa.

Ya yi kira ga al’ummar kasar nan da kada su yarda a rika zagin Shugaba Kasa da ma’aikatan hana fasakwauri, kan wannan aiki da ake yi na hana shigo da miyagun abubuwa zuwa kasar nan.

Ya ce babu shakka miyagun kwayoyin da ake shigo da su kasar nan, suna cutar al’ummar kasar nan, don haka ya kamata jama’a su yi tunani kan wannan al’amari.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin